Majalisar Dattijan Nijeriya na son a tsagaita wuta a Gaza

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattijan Nijerya ta buqaci gwamnatin tarayyar ƙasar ta haɗa kai da wasu ƙasashe domin yin kira a tsagaita buɗe wuta a rikicin Isra’ila da Hamas.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne sojojin Isra’ila suke yin ruwan bama-bamai a Gaza, bayan mayaqan Hamas sun ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 a Isra’ila, waɗanda mafi yawansu fararen hula ne, a cewar hukumomin Isra’ila.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas, adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya zarce mutum 10,000 ciki har da yara sama da 4,000.

A wani ƙudiri da Sanata Abdulrahman Kawu daga Kano ta Kudu ya gabatar a ranar Talata, Majalisar Dattawar bayan muhawara mai zurfi ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra’ila da Hamas a matsayin abin tsoro.

Yayin da suke bayyana ra’ayinsu, ‘yan majalisar sun yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a ɓangarorin biyu, sannan suka buƙaci a zauna lafiya domin kauce wa abin da zai kawwo yaɗuwar rikicin.

Wannan kiran na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta qara jaddada buƙatar tsagaita wuta cikin gaggawa, inda ta bayyana Gaza a matsayin maƙabarta ga ƙananan yara yayin da adadin waɗanda suka mutu ya haura 10,000.