Yadda shari’ar “Farmgate” ke barazana ga makomar shugaban Afirka ta Kudu

Spread the love

A yayin da siyasar Afirka ta Kudu ke ƙara shiga wani sabon yanayi mai cike da tashin hankali, shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa, na fuskantar ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa tun bayan hawansa mulki a shekarar 2018. Wannan na zuwa ne bayan sake farfaɗo da batun tsige shi daga mulki sakamakon wata badaƙala da aka fi sani da “Farmgate” lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce mai girma kan maƙudan kuɗaɗen ƙasashen waje da aka ce an ɓoye a cikin kujera a gonarsa.

Rahotanni sun nuna cewa barayin da suka shiga gonar shugaban ƙasar sun yi awon gaba da dubban daloli da aka ajiye a cikin kayan ɗaki, lamarin da ya haifar da tambayoyi masu yawa daga jama’a, ‘yan siyasa da kuma masana shari’a. Tun daga lokacin, batun ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka mamaye siyasar ƙasar.

Ko da yake Ramaphosa ya ci gaba da musanta aikata wani laifi, matsin lambar siyasa da kuma hukuncin kotu sun sake buɗe ƙofar yiwuwar fara cikakken tsarin tsige shi daga mulki.

Dokar kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu ta bai wa majalisar dokoki ikon cire shugaban ƙasa daga mulki idan aka same shi da karya kundin tsarin mulki, aikata babban laifi, ko kuma rashin iya gudanar da ayyukansa.

Tsarin yana farawa ne idan wani ɗan majalisa ya gabatar da ƙudirin neman tsige shugaban ƙasa. Daga nan ne kakakin majalisar zai miƙa batun ga wani kwamiti mai zaman kansa da ya kunshi masana harkar shari’a domin su tantance ko akwai hujjojin da za su iya tabbatar da zargin.

Idan kwamitin ya tabbatar akwai buƙatar ci gaba da bincike, ‘yan majalisa za su kaɗa ƙuri’ar ko za a fara shari’ar tsige shugaban ƙasar. Idan aka amince, za a kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da zurfaffen bincike kan zarge-zargen.

A ƙarshe, idan kwamitin ya ba da shawarar a tsige shugaban, majalisar za ta sake kaɗa ƙuri’a. Sai dai dole ne kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisa su amince kafin shugaban ƙasa ya rasa muƙaminsa.

Jam’iyyar African National Congress (ANC) ta Ramaphosa na da kujeru 159 cikin 400 a majalisar dokokin ƙasar. Duk da cewa wannan ba rinjaye kai tsaye ba ne, jam’iyyar na mulki ne cikin haɗaka da Democratic Alliance da wasu ƙananan jam’iyyu.

Wannan na nufin idan dukkan ‘yan majalisar ANC suka tsaya tare da shugaban ƙasar, zai iya tsallake duk wata ƙuri’ar tsige shi. Amma masana siyasa na gargaɗin cewa rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar na iya sa wasu su juya masa baya.

Masaniyar siyasa Susan Booysen ta bayyana cewa duk da Ramaphosa na da goyon baya, ba za a iya kawar da yiwuwar samun masu bore daga cikin jam’iyyarsa ba, musamman idan matsin lamba daga jama’a ya ƙara tsananta.

Jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), wacce ke daga cikin manyan jam’iyyun adawa masu tsananin suka ga gwamnatin Ramaphosa, ta kai karar matakin majalisar zuwa kotun tsarin mulki.

A watan Mayun 2026 ne kotun ta yanke hukuncin da ya sake farfado da tsarin tsige shugaban ƙasar. Wannan hukunci ne da ya sake jefa siyasar ƙasar cikin wani sabon yanayi mai cike da rashin tabbas.

Bayan hukuncin, majalisar ta sanar cewa kakakin majalisa zai fara ɗaukar matakan kafa kwamitin bincike na tsige shugaban ƙasar, ko da yake ba a bayyana lokacin da aikin zai kammala ba.

A gefe guda kuma, Ramaphosa ya bayyana cewa zai ƙalubalanci rahoton kwamitin farko a kotu, matakin da masana ke ganin zai iya jinkirta tsarin.

Baya ga tsarin tsige shugaban ƙasa, Ramaphosa na kuma fuskantar yiwuwar kaɗa kuri’ar rashin amincewa da shi.

Saboda irin wannan kuri’a na bukatar rinjaye mai sauki ne kawai, wato fiye da rabin kuri’un ‘yan majalisa hakan na nufin shugaban ƙasar zai buƙaci cikakken goyon bayan abokan hadakarsa domin tsira.

Jam’iyyun uMkhonto weSizwe (MK) da African Transformation Movement (ATM) sun riga sun gabatar da buƙatar gudanar da ƙuri’ar rashin amincewa da shugaban ƙasar. Sai dai har yanzu majalisar ba ta bayyana ko za ta amince da bukatar ba.

Masu sharhi na ganin wannan rikici na iya zama ɗaya daga cikin manyan jarrabawar dimokuradiyyar Afirka ta Kudu tun bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

Yayin da ANC ke ƙoƙarin kare shugabanta, jam’iyyun adawa na ƙoƙarin amfani da damar wajen raunana gwamnatin da suka daɗe suna zargi da rashawa da gazawa.

Wasu masana na gargadin cewa duk wani rikici mai tsawo kan shugabancin ƙasar na iya shafar tattalin arziki, zuba jari da kuma martabar Afirka ta Kudu a duniya.

Sai dai a yanzu, tambayar da ta fi ɗaukar hankalin jama’a ita ce: Shin Cyril Ramaphosa zai iya tsallake wannan guguwar siyasa kamar yadda ya tsallake ƙalubale a baya, ko kuwa “Farmgate” zai zama abin da zai kawo ƙarshen mulkinsa?

By ukarofi