‘Yan sanda sun tabbatar da halaka jami’ai 17 bayan mummunan hari a Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan Sanda ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda 17 a sakamakon mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai a Makarantar Horar da Dakarun Leken Asiri ta Sojin Ƙasa da ke yankin Buni Yadi a karamar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Jami’an, wadanda ke can domin samun horo na musamman, sun rasu ne lokacin da ‘yan ta’adda suka far wa makarantar ta fuskoki daban-daban da misalin ƙarfe 1:15 na daren ranar 8 ga watan Mayu, 2026.

Haka kuma, wasu jaruman sojojin ƙasa ma sun rasu a yayin da suke maida martani ga hararin.

Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana jami’an da suka riga mu gidan gaskiya a matsayin jajirtattu masu kishin kasa, sannan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalansu tare da ba su tabbacin cewa ba za a taba mancewa da sadaukarwar da suka yi ba.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin ya ziyarci makarantar inda ya yi ta’aziyya ga Kwamandan makarantar, Birgediya Janar A.C. Enuagu, da sauran jami’an da suka tsira, inda ya karfafa musu gwiwa su kammala horon domin karrama abokan aikinsu.

A ƙarshe, IGPn ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar, tare da haɗin-gwiwar dakarun soji, za su cigaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji