
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sashen Dakarun Sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ya fitar da bidiyon atisayen sojoji da ya yi ajalin kwamandan ISIS Abu-Bilal Al-Manuki.
A wata sanarwa da AFRICOM ya fitar a ranar Asabar, an ce an gudanar da atisayen ne a ƙarƙashin umarnin Shugaban Amurka da Sakataren Yaƙi da kuma haɗin-gwiwar gwamnatin Nijeriya.
An ruwaito cewa, bincike ya ya nuna cewa an halaka ‘yan ta’adda da dama a yayin harin.
Sashen ya harin ya nufi yankin da akwai taron mambobin ISIS a arewa maso gabashin Nijeriya, inda ya bayyana shi a matsayin wani ɓangare na yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
Al-Manuki na ɗaya daga cikin mayaƙan ISIS da ke aiki tsakanin ƙasa-da-ƙasa a fannin yaɗa labarai da samar da kuɗaɗe da kuma ci-gaba a harkokin samar da makamai, ababen fashewa da tankunan yaƙi.
Ana ɗaukar sa a matsayin ɗan ta’adda mafi aiki a duniya, wanda ya ƙware wajen shirya ƙaddamar da hare-hare da bayar da umarnin garkuwa da mutane.
