Afirka ta Kudu: Johannesburg na fuskantar barazanar katse wutar lantarki saboda bashin biliyoyin kuɗaɗe

Spread the love

Birnin Johannesburg, wanda ake kallonsa a matsayin zuciyar tattalin arzikin South Africa, ya shiga wani sabon yanayi mai tayar da hankali bayan kamfanin samar da wutar lantarki mallakin gwamnati, Eskom, ya yi barazanar rage ko ma katse wutar lantarkin da yake bai wa birnin saboda tarin bashin da ya ce gwamnatin birnin ta kasa biya tsawon lokaci.

Kamfanin Eskom ya bayyana cewa birnin Johannesburg tare da kamfanin rarraba wutar lantarki na birnin mai suna City Power suna bin sa bashin rand biliyan 5.26, kwatankwacin dala miliyan 315. Haka kuma akwai wani ƙarin bashin rand biliyan 1.58 da ya kamata a biya kafin ranar 5 ga watan Yuni.

Lamarin ya sake jefa hankulan jama’a cikin fargaba musamman ganin yadda matsalar wutar lantarki ta daɗe tana addabar ƙasar, abin da ya janyo tangarɗa ga masana’antu, ƙaruwar rashin ayyukan yi da kuma tsadar rayuwa ga talakawa. Johannesburg dai na ɗaya daga cikin biranen da tattalin arzikin ƙasar ya fi dogaro da su, saboda tarin kamfanoni, bankuna da cibiyoyin kuɗi da ke cikinsa.

A cikin sanarwar da ya fitar, Eskom ya ce ya riga ya aika da gargaɗin cewa yana shirin “ragewa, katsewa ko dakatar da samar da wutar lantarki” zuwa wasu manyan wuraren da ke bai wa birnin wuta idan har ba a samu warware matsalar bashin ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai gwamnatin Johannesburg ba ta mayar da martani kan tambayar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya aika mata ba.

Kamfanin Eskom ya kuma bayyana cewa sama da shekara biyu kenan yana tattaunawa da hukumomin birnin domin nemo mafita kan matsalar bashin, amma duk da yarjejeniyoyi da aka yi, birnin na ci gaba da kasa cika alƙawuran biyan kuɗaɗen.

Wannan rikici ya zo ne a lokacin da hukumomin baitul malin ƙasar suka fara nuna damuwa mai tsanani kan yadda harkokin kuɗaɗen Johannesburg ke ƙara taɓarɓarewa. A baya-bayan nan ma ma’aikatar kuɗi ta ƙasar ta yi gargadin cewa matsalar kuɗin birnin na iya haddasa matsala ga ayyukan jama’a da gudanarwar birnin baki ɗaya.

Masana tattalin arziki na ganin idan aka rage wutar lantarki a Johannesburg, hakan zai iya haddasa babbar matsala ga dubban kamfanoni tare da ƙara jefa ƙasar cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Sai dai duk da irin matsalolin da Eskom ya daɗe yana fama da su na basussuka da ƙarancin samar da wuta, kamfanin ya fara nuna alamun farfaɗowa bayan tallafin gwamnati da kuma ingantuwar ayyukan tashoshin wutar kwal da yake amfani da su. A bara ma kamfanin ya sanar da samun ribarsa ta farko cikin shekaru takwas.

By ukarofi