Somaliland mai neman ɓallewa daga Somalia ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za ta buɗe ofishin jakadancinta a birnin Jerusalem, bayan Israel ta zama ƙasa ta farko da ta amince da ita a hukumance a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Jakadan Somaliland, Mohamed Hagi, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin ɗ, inda ya ce matakin wani ɓangare ne na sabuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin ɓangarorin biyu. A cewarsa, Isra’ila ita ma za ta buɗe ofishin jakadancinta a babban birnin Somaliland wato Hargeisa.
Tun a watan Disamban bara ne Isra’ila ta sanar da amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ‘yanci da cikakken iko. Sai dai matakin ya fusata Somalia wadda ta bayyana shi a matsayin hari kai tsaye kan ikon ƙasarta da haɗin kan yankinta.
Somaliland dai ta shafe shekaru tana gudanar da harkokinta cikin ‘yanci tun bayan rugujewar gwamnatin Somalia a shekarar 1991 lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke. Duk da zaman lafiyar da yankin ya samu idan aka kwatanta da sauran sassan Somalia, ƙasashen duniya sun daɗe ba sa amincewa da ita a hukumance.
A tsawon shekaru, Somalia na ci gaba da matsa lamba ga ƙasashen duniya domin hana su amincewa da Somaliland. Amma masana harkokin siyasa na ganin matakin Isra’ila na iya buɗe ƙofar sababbin alaƙoƙin diflomasiyya ga Somaliland tare da ƙara mata damar shiga kasuwannin duniya.
Ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya bayyana cewa buɗe ofishin jakadancin Somaliland a Jerusalem zai zama wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Idan aka buɗe ofishin, zai zama jakadanci na takwas da ke Jerusalem, birnin da ke ci gaba da zama cibiyar rikicin siyasa tsakanin Isra’ilawa da Falasɗinawa. Yawancin ƙasashen duniya har yanzu suna da ofisoshin jakadancinsu ne a Tel Aviv saboda rashin amincewa da ikirarin Isra’ila cewa Jerusalem gaba ɗaya babban birninta ne.
