Sarkin Argungu ya buƙaci mazauna su tanadi makamai a hukumance don kariya ga ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‎Sarkin Argungu, Muhammad Samaila-Mera ya kirayi al’ummar yankinsa da su mallaki makamai ta hanyar da doka ta tanada don ƙara karfin tsaro na gida da kuma kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Haka kuma, ya buƙaci ƙauyukan da ke ƙarƙashin masarautarsa da kasancewa masu kula da sanya ido akan ayyukan ‘yan ta’adda da kan kai musu farmaki akai-akai, yana mai cewa ɗaukar matakin kare kai ta halastaccen hanya shi ne ya daci a matsayin lalura ga cigaba da taɓarɓarewar lamuran tsaro.

‎Sarkin ya bayyana haka ne a yau Jumma’a yayin wani taro tare da hakimai, dagatai, da masu unguwanni a fadarsa da ke Argungu.

Samaila-Mera ya jaddada buƙatar al’umma su ƙarfafa salon tattara bayanan sirri tare da gaggauta raba wa hukumomin tsaro bayannan da za su taimaka musu a ƙoƙarin magance matsalolin rashin tsaro da ke cigaba da addabar al’umma.

Kazalika, ‎ya shawarci mazauna yankin da su haɗa kai wajen samar da albarkatu don siyan makamai da gwamnati ta amince da su don kariyar kai a dokance.

By Babaji

Leave a Reply