Matatar Ɗangote ta ƙara adadin samar da fetur zuwa ganga 700,000 a kullum

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin matatar man Fetur ta Ɗangote ta sanar da ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai daga ganga 650,000 zuwa ganga 700,000 a kowace rana.

Rahotanni sun bayyana cewa matatar ta riga ta gudanar da gwajin aiki inda ta tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a rana, abin da ya zarce ƙarfin da aka tsara mata tun farko na ganga 650,000 a kullum.

A cewar matatar, hakan na nuna ingancin tsarin injiniyoyinta da kuma yadda take aiki yadda ya kamata domin wadatar da masu amfani da fetur a Nijeriya.

A baya ne Mataimakin Shugaban kamfanin mai da gas na Ɗangote, Devakumar Edwin ya bayyana cewa ana shirin faɗaɗa matatar zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekaru masu zuwa, lamarin da zai iya sa ta zama ɗaya daga cikin mafi girman matatun mai a duniya, tare da ƙara wa Nijeriya da Afirka tasiri a kasuwar makamashi ta duniya.

Matatar, wadda ita ce mafi girman matatar mai a duniya, ta fara aiki ne a shekarar 2024 kuma tana samar da fetur, dizal da man jiragen sama domin kasuwannin cikin gida da na wasu ƙasashe.

By Babaji

Leave a Reply