Tsauraran sharuɗɗan beli sun saɓa wa doka – NBA ga kotuna

Spread the love

Ƙungiyar Lauyoyin Ƙasa (NBA) ta nuna damuwa akan yadda wasu kotuna da jami’an tsaro ke sanya tsauraran sharuɗɗan beli da ke hana mutane da dama cin gajiyar ‘yancin da doka ta tanada a gare su.

NBA ta yi kira ga kotuna da hukumomin tsaro da su sake duba tsarin bayar da beli domin tabbatar da adalci da kare haƙƙin waɗanda ake tuhuma.

Shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe ya bayyana cewa yawan sanya sharuɗɗan da suka haɗa da buƙatar manyan ma’aikatan gwamnati ko masu kadarori masu tsada a matsayin masu tsaya wa wanda ake tuhuma na hana mutane da dama samun beli duk da cewa an amince musu da shi.

A cewarsa, irin waɗannan sharuɗɗa sun mayar da beli tamkar wata hanya ta ci gaba da tsare mutum kafin a yanke masa hukunci, lamarin da ya saɓa wa ƙa’idar adalci da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Ya jaddada cewa a ƙarƙashin doka, ana ɗaukar wanda ake tuhuma a matsayin mara laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka, don haka bai kamata a sanya masa sharuɗɗan da ba zai iya cikawa ba kafin a ba shi ‘yanci.

Osigwe ya ƙara da cewa manufar beli ita ce tabbatar da halartar wanda ake tuhuma a gaban kotu idan an buƙace shi, ba hukunta shi kafin a same shi da laifi ba.

Kazalika, NBA ta kuma buƙaci kotuna da su riƙa tabbatar da cewa kowane sharaɗin beli da za a gindaya ya kasance mai sauƙi, adalci da wanda ake tuhuma zai iya cikawa ba tare da wata wahala mai tsanani ba.

By Babaji

Leave a Reply