Borno: Sojoji sun ceto mai shayarwa, jariri da wasu daga cikin ‘yan Ngoshe da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na ƙarƙashin Atisayen HAƊIN KAI (OPHK) sun ƙara kaimi wajen murƙushe ayyukan ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabas, bayan aun wasu nasarori da suka haɗa da ceto mutanen da aka sace gami da kuma tilasta wa ‘yan ta’adda miƙa wuya.

An ƙaddamar da atisayen ne a yankin Amuda, inda dakarunmu suka yi nasarar ceto wata mata mai suna Maryam Muhammad (shekara 20) da ɗanta ƙarami, Bello Muhammad, waɗanda aka yi garkuwa da su tun a ranar 3 ga watan Maris, 2026 a garin Ngoshe.

Bayan tserewar da suka yi daga maboyar ta’addancin sakamakon hare-haren sojoji, an duba lafiyarsu kafin a sake haɗa su da iyalansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wannan nasara ta ai ne yayin wani samame na musamman da haɗin-gwiwar jami’an Civilian JTF a yankunan Wulgo, Gumsari, da Hausari da sojoji suka gano tare da lalata su.

Haka kuma, dakarun sun yi nasarar ƙwato wasu daga cikin kayayyakin ayyukan jinya ciki har da jini da magunguna, harsasai da kayan amfanin gida na wani babban kwamandan ‘yan ta’adda da ake kira Amir.

A sakamakon matsin lamba a tsaunukan Mandara, wasu iyalan ‘yan ta’addan sun yanke shawarar miƙa wuya ga dakarun soji a Gwoza da kan hanyar Gwoza zuwa Limankara domin neman tsira, waɗanda a yanzu, ana gudanar da bincike da tantance su kamar yadda doka ta tanadar.

By Babaji

Leave a Reply