Rikicin siyasa tsakanin Amurka da Italiya na ƙara tsananta

Spread the love

*Trump ya soki Meloni, ya ce ya yi mamaki da halinta

*Firaministar ta ce ta dawo daga rakiyar Trump kan yaƙi da Iran 

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Firaministar Italiya Giorgia Meloni, yana mai cewa ta nuna rashin jaruntaka kuma ta ba Amurka kunya, a wani mataki da ya girgiza dangantakar siyasa tsakanin ƙasashen biyu.

Meloni, wadda a baya ta kasance mai goyon bayan Trump, ta fara nesanta kanta da shi bayan yaƙin Iran, sannan ta soki kalaman da Trump ya yi kan Paparoma Leo, tana kiran su marasa dacewa.

Trump ya mayar da martani cikin hira da jaridar Corriere della Sera, yana mai cewa Meloni ta bambanta da yadda ya zata, yana mai cewa ya yi mamaki da ita.

Ya kuma zarge ta da ƙin taimakawa wajen buɗe mashigar Hormuz, yana mai cewa tana son Amurka ta yi mata aikin.

Fadar White House da ofishin Meloni sun ƙi yin tsokaci kai tsaye, amma ’yan siyasar Italiya daga ɓangarori daban-daban sun fito suna kareta.

Ministan harkokin waje Antonio Tajani ya jaddada cewa Italiya na goyon bayan haɗin kan yammacin duniya, amma wannan haɗin kai dole ne ya ginu kan mutunta juna.

Wannan suka na Trump ya nuna sauyi mai girma, musamman ganin cewa Meloni ita ce kadai shugabar Turai da ta halarci rantsar da shi a 2025.

Trump ya kuma zarge ta da rashin damuwa da yiwuwar Iran ta mallaki makamin nukiliya, yana cewa hakan na iya jefa Italiya cikin haɗari.

Meloni na fuskantar matsin lamba daga cikin gida bayan faɗuwar kuri’ar raba gardama kan gyaran shari’a, da kuma saukar abokinta Viktor Orban daga mulki a Hungary.

Haka kuma tashin farashin makamashi da yaƙin Gulf na ƙara jefa tattalin arzikin Italiya cikin matsala, wanda ya sa jama’a ke nuna rashin goyon baya ga rikicin.

Meloni ta ƙi barin jiragen yaƙin Amurka su yi amfani da sansanin soja a Sicily, sannan ta dakatar da yarjejeniyar soji da Isra’ila.

Trump ya ce Italiya na fama da tsadar makamashi amma har yanzu ba ta shirya taimakawa wajen buɗe mashigar Hormuz ba.

By ukarofi