Yunwa ta sanya Falasɗinawa fara cin wata ciyawa a matsayin abinci

Sakamakon ƙarancin abinci da kuma barazanar ɓarkewar yunwar ga al’ummar Falasɗinawa, hakan ya tilasta wa wasu da dama dafa ganyen wani haki da suke kira da Khubaiza, don ci a matsayin abinci.

Wani magidanci Mohammad Shehadeh ya ce, ya na yin kasada da rayuwarsa ne wajen ɗebo ganyen don ciyar da iyalansa da kuma sayarwa a kasuwa.

Ita ma Maryam Al-Attar da ta ce sojojin Isra’ila sun tava harbin su ita da mai gidanta a lokacin da su ka je ɗebo ciyawar ta Khubaiza a gabashin Gaza, ta ce lokacin da ƙananan ‘ya’yanta suka ce mata suna jin yunwa, hankalinta ya tashi saboda rashin abin da za ta ba su, sai daga bisani ta ba su wannan ciyawa a matsayin abinci.

‘Ya’yana mata suka ce mani, mama za mu ci abinci, zuciyata ta karye babu abin da zan ba su koda guntun burodi, na je na ɗebo ciyawar ta Khubaiza. A yanzu muna iya samun ciyawar, amma a nan gaba fa, daga ina za mu samu?” Inji matar.

Al’ummar yankin Gaza dai sun shiga cikin wani mawuyacin yanayi ne bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a cikinsa, wanda ke zaman ramuwar gayya kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

A tsakiyar watan Maris ɗin nan ne, wata ƙungiya da ke sa ido kan al’amuran da suka shafi yunwa a duniya, ta ce nan da watan Mayu mai zuwa, akwai yuwuwar samun ɓarkewar annobar yunwa a Arewacin Gaza, wata kila ta mamaye yankin bakiɗaya a watan Yuli.

Ƙasashe da dama na ta kiraye-kirayen ganin an tsagaita wuta a Gaza, inda ma daga cikin matakan da ya sa Kwamitin Tsaro na Majalisa Ɗinkin Duniya ɗaukar matakin kaɗa ƙuri’ar neman tsagaita wuta a Gaza a ranar Litinin, har da batun samun damar shigar da kayan agaji yankin.