Zan bayyana makomata bayan gasar kofin Turai – Mbappe

Sga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya ce zai bayyana matsayarsa na gaba bayan gasar kofin nahiyar Turai ta 2024.

Ɗan wasan na Faransa ya yi magana a karon farko game da raɗe-raɗin da ake yi na yarjejeniyarsa da Real Madrid a bazara.

A yayin da yake magana a gidan jaridar Faransa, ya ce “Ban sanar da komai ba saboda babu abin da zan sanar.

“Zan bayyana makomata kafin gasar kofin Turai.”

Dangane da gasar Olympics ta Paris, Mbappe ya ce: “A koyaushe ina da wannan buri, abu ne na musamman kuma a koyaushe ina cewa zan so zuwa wurin, amma sai dai yadda yanayi ya ba da.

“Ina da kwantiragi da Paris Saint Germain kuma a halin yanzu kulob ɗin bai sanar da ni komai ba, domin ba mu yi magana a kai ba.”