Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da aƙida – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dr Abdullahi Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya ce jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da asali da aƙida, wanda ke haifar da sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya ƙaddamar da kodinetocin jam’iyyar na shiyyoyi a faɗin ƙasar nan.

Ya ce dole ne lamarin ya canza da kyau.

Ya ce kodinetocin shiyyar ne za su kula da shiyyoyin siyasa shida na ƙasar nan.

Gwamna Ganduje ya naɗa Gwamna Hope Uzodimma na Imo a matsayin kodinetan shiyyar Kudu Maso Gabas, yayin da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara shi ne kodinetan shiyyar Arewa ta Tsakiya, da kuma Gwamna Mai Mala Buni kodinetan na shiyyar Arewa maso Gabas.

Ya kuma naɗa Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna a matsayin kodinetan Arewa maso Yamma, yayin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu wanda ke aiki a matsayin kodinetan Kudu maso Yamma da Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba a matsayin kodinetan Kudu maso Kudu.

Gwamna Ganduje ya ce ana sa ran gwamnonin za su fara tattaunawa da shugabannin jam’iyyar lokaci-lokaci.

“Ya kamata su haɗa kai da jam’iyyar don fara aiwatar da sulhu na gaskiya ga mambobin da aka saɓa mawa a yankin siyasa.

“Kwaɗaitar da gwamnonin shiyyar domin su shiga cikin ayyukan jam’iyyar yadda ya kamata a shiyyar, tuntuɓar gwamna da warware matsalolin da za su ƙara bunƙasa ci gabanta da haɗin kanta.

“Haka zalika su taimaka wa jam’iyyar kan tattara albarkatun ƙasa wajen yi wa jam’iyyar hidima da kuma shiga duk wani aiki da jam’iyyar za ta iya ba ta,” inji shi.

“Muna so mu canza labari, muna son jam’iyyarmu ta siyasa ta kasance mai aiki a cikin shekara, saboda haka, dukkanin ofisoshinmu dole ne su kasance masu aiki a jiki, dukkanin ofisoshinmu dole ne su kasance masu aiki.

“Tun daga ƙananan hukumomi zuwa matakin jiha, dole ne a gudanar da ayyuka a ko’ina, amma hakan ba zai iya faruwa kwatsam ba,” in ji shi.

Da yake mayar da martani, Mista Uzodimma, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba, PGF, ya bayyana jin daɗinsa tare da yabawa shugabannin jam’iyyar kan wannan shiri.

“Mun yi matuqar farin ciki da farin ciki cewa jam’iyyar a cikin hikimarta ta vullo da wannan sabuwar manufa ta haɗin kai, mu a PGF muna da gwamnoni 20 wanda ke nufin jihohi 20 ne APC ke mulki a halin yanzu.

“Dole ne mu fara daga nan don tabbatar da haɗin kan dukkan ‘ya’yan jam’iyyarmu, kuma mu kai ga gaci, ina ganin wannan ita ce hikimar da ke tattare da ƙaddamarwar,” in ji Mista Uzodimma.