Ko a mayar da ni nan da kwana bakwai ko mu haɗu a kotu – Sanata Ningi ga Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ahmed Ningi, ya rubutawa shugaban majalisar, Godswill Akpabio wasiƙa, yana neman a ɗage dakatarwar da aka yi masa.

Ningi, wanda ya rubuta wa Akpabio wasiƙa ta hannun lauyansa, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa idan ba a ɗage dakatarwar da aka yi masa ba nan da kwanaki bakwai masu zuwa zai kai majalisar dattawa gaban babbar kotun tarayya.

Majalisar dattawa, a ranar 12 ga watan Maris, ta aika wa Ningi dakatarwar watanni uku saboda iƙirarin da ya yi na cewa an yi cushe a kasafin kuɗin 2024 har na Naira tiriliyan 3.7.

Ningi, a wata hira da ya yi da manema labarai, ya yi iƙirarin cewa kasafin da majalisar ƙasa ta zartar na kasafin shekarar 2024 ya kasance N25tn, wanda Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe ya kai N28.7tn.

Sai dai a zaman majalisar da aka yi a ranar 12 ga watan Maris, majalisar dattawan ta kai Sanatan Bauchi domin kare wannan zargi, inda daga ƙarshe aka yi masa hukuncin dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni uku saboda ɓata sunan majalisa bisa abin da sanatoci suka yanke shawarar cewa ba shi da tushe balle makama.

Sanata Ningi daga nan ya sauka daga muƙaminsa na Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa inda aka maye gurbinsa da Sanata Abdulaziz Yar’Adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a jam’iyyar All Progressives Congress.

“Ba ku gamsu da hirar ba, kun sa aka gurfanar da wanda muke karewa a gaban Majalisar Dattawa a ranar 14 ga Maris, 2024 saɓanin tanadin dokar Majalisar Dokoki (Powers and Privileges), 2018.”

Falana, a cikin wasiƙar, ya ce shugaban majalisar dattijai ya yi aiki a matsayin mai tuhuma, mai gabatar da ƙara da kuma alƙali a shari’ar, yana mai cewa hakan ya saɓawa tanadin sashe na 36 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.”

Falana ya ƙara da cewa, baya ga tauye haƙƙin Ningi na yin adalci, majalisar ta kuma take haƙƙin al’ummar mazaɓar Bauchi ta tsakiya na samun wakilci a majalisar na tsawon watanni uku.

“Wannan saɓawa sashe na 111 na Kundin Tsarin Mulki da Mataki na 13 na Kundin Tsarin ‘Yancin Ɗan Adam na Afirka,” in ji SAN.

“Kamar yadda kuka sani, babbar kotun tarayya ta yi fatali da dakatarwar da aka yi wa wasu ‘yan majalisar dattawa da na wakilai da ke zargin shugabannin majalisun biyu da karkatar da kasafin kuɗi, ko cin hanci da rashawa ko kuma yin amfani da muƙamai.

“Musamman, kotu ta bayyana dakatar da ‘yan majalisar da abin ya shafa ya saɓawa ƙa’ida.

“A matsayinka na babban lauya, ya kamata kai (Akpabio) ya jawo hankalin ‘yan majalisar dattawa kan wadannan hukunce-hukunce da wasu da dama inda manyan kotunan wasu jihohi da kotun ɗaukaka qara suka ce babu wata majalisa a Nijeriya da ke da iko. a dakatar ko korar dan majalisa da ƙwace masa albashi da alawus alawus.

“Saboda abubuwan da suka gabata, zaku yarda da mu cewa dakatarwar da aka yi wa Sanata Ningi da kuma hana shi haƙƙinsa ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya sava wa kundin tsarin mulki a kowane abu.

“Duk da haka, idan har kuka kasa amsa buƙatarmu kwana bakwai bayan samun wannan wasiƙa, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen shigar da ƙara babbar kotun tarayya don ta maido da wanda muke karewa. Hakazalika za mu kai rahoton ku ga kwamitin ladabtar da masu aikin shari’a kan yadda suka bi hukunce-hukuncen babban kotun tarayya da na kotun ɗaukaka ƙara da raini.”