DHQ na neman Farfesa da wasu mutum 7 ruwa a jallo bisa zargin kashe sojoji a Delta

Daga BASHIR ISAH

Babban Ofishin Tsaro (DHQ) da ke Abuja, ya ce yana beman wasu mutum 8, ciki har da Farfesa kan zarginsu da hannu cikin kashe sojoji 17 da aka yi kwanan nan a yankin Okuama, Jihar Delta.

A ranar Alhamis Ofishin ya bayyana sunaye da hotunan waɗanda yake farauta ɗin domin jama’a su taimaka da bayanan da za su taimaka a damƙe su.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da: Alevwru Daniel, Farfesa Ekpokpo Arthur, Andaowe Deniss Bakriri, Igboli Ebi, Akata Malawa David, Sinclear Oliki, Clements Okoli, Oghenerhukehve da kuma Rueben Baru.