Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tinubu ta ware N90bn don cikata wa maniyyata kuɗin Hajji

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta ware Naira biliyan 90 domin cikata wa maniyyata kuɗin Hajjin Bana.

Tallafin na zuwa ne biyo bayan ƙarin kuɗin Hajji da aka yi bayan sama da Naira miliyan huɗu da maniyyatan suka yi da farko.

A farkon wannan makon ne Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ba da sanarwar cewa, an yi ƙarin kuɗin Hajjin bana da Naira Miliyan 1.9 wanda kuma ake buƙatar kowane maniyyaci ya biya a cikin ƙankanin lokaci ko kuma ya haƙura da tafiya Hajji bana.

Tun bayan sanarwar ƙarin da NAHCON ta yi, wasu jihohi sun yi yunƙurin cikata wa maniyyatansu kuɗin, ciki har da Jihar Ribas da Kano.

MANHAJA ta kalato cewar, tallafin na Gwamnatin Tarayya zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙe wa maniyyatan bana daga Nijeriya nauyin da ke kansu na kuɗi.