Cikakken bayanin yadda Tinubu ya kafa Majalisar Havaka Tattalin Arzikin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin tafiyar da tattalin arzikin qasa da tabbatar da tsayayyen tsare-tsare da aiwatar da tattalin arzikin ƙasa cikin aminci, Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ya kafa Kwamitin Kula da Tattalin Arzikin Ƙasa na Shugaban Ƙasa (PECC) da kuma samar da Ƙungiyar Kula da Tattalin Arziki ta Gaggawa (EET).

A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafen yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, kwamitin kula da tattalin arzikin shugaban ƙasa (PECC) ya ƙunshi fitattun shugabanni da manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da:

(1) Shugaban Tarayyar Nijeriya – Shugaban Hukumar PECC
(2) Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya – Mataimakin Shugaban PECC da NEC
(3) Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya
(4) Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya
(5) Ministan tattalin arziki da kuma ministan kuɗi
(6) Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
(7) Ministan Noma da Tsaron Abinci
(8) Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya
(9) Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki
(10) Ministan Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arziki na Dijital
(11) Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari
(12) Ministan Qwadago da Samar Da Ayyukan yi
(13) Ministan Ruwa da Tattalin Arziki
(14) Ministan Wutar Lantarki
(15) Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur
(16) Ƙaramin Ministan Gas
(17) Ministan Sufuri
(18) Ministan Ayyuka
Kwamitin na PECC zai kuma ƙunshi manyan mambobi na kamfanoni masu zaman kansu, tare da sauran mambobi da za su yi aiki na tsawon shekara guda, bisa ga umarnin shugaban ƙasa:
(1) Alhaji Aliko Dangote
(2) Mr. Tony Elumelu
(3) Alhaji Abdulsamad Rabiu
(4) Malama Amina Maina
(5) Malam Begun Ajayi-Kadir
(6) Madam Funke Okpeke
(7) Dr. Doyin Salami
(8) Mr. Patrick Okigbo
(9) Malam Kola Adesina
(10) Mr. Segun Agbaje
(11) Malam Chidi Ajaere
(12) Malam Abdulkadir Aliu
(13) Malam Rasheed Sarumi

Bugu da ƙari, a cikin ƙudirinsa na magance matsalolin tattalin arziki cikin hazari da kuma tabbatar da ingantaccen aiwatar da dabarun tattalin arziki, Shugaba Bola Tinubu ya kafa Ƙungiyar Kula da Tattalin Arziki ta Gaggawa (EET) tare da umarni aiwatar da tsarin tattalin arziki cikin gaggawa.

Ƙungiyar ta ƙunshi manyan jami’an gwamnati da shugabannin masana’antu don haɓaka tsarin haɗin gwiwar shugaban aasa don samun ƙarfin tattalin arziki da cigaba. A yanzu an wajabta wa EET gabatar da wani cikakken tsari tattalin arziki na shekarar 2024 ga kwamitin PECC, wanda ya ƙunshi watanni shida masu zuwa, don aiwatarwa cikin gaggawa cikin makonni biyu da ƙaddamar da ita. EET za ta haɗu sau biyu a mako kuma ta ƙunshi mambobi kamar:

(1) Ministan Tattalin Arziki kuma Ministan Kuɗi (Shugaban EET)
(2) Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki
(3) Ministan Wutar Lantarki
(4) Ministan Noma da Tsaron Abinci
(5) Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a
(6) Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari
(7) Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
(8) Mai Ba Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro
(9) Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya
(10) Gwamnan jihar Anambra
(11) Gwamnan jihar Ogun
(12) Gwamnan Jihar Neja
(13) Shugaban Ma’aikatar Harajin Cikin Gida ta Tarayya
(14) Darakta-Janar, Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya
(15) Shugaban Kamfanin NNPC
(16) Shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Nijeriya
(17) Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Makamashi
(18) Dr. Bismarck Rewane, Masanin Tattalin Arziki
(19) Dr. Suleyman Ndanusa, masanin tattalin arziki

Tawagar Gudanar da Tattalin Arziki, wacce aka kafa a watan Oktoba 2023, kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki da kuma Ministan Kuɗi ke jagoranta, tana aiki a matsayin ƙungiya a ƙarƙashin Kwamitin Gudanar da Tattalin Arziƙi na Shugaban Ƙasa (PECC), suna taka muhimmiyar rawa a tsarin tafiyar da tattalin arzikin da aka kafa. EMT a al’adantu wajen ƙirƙirar hanyoyin havaka tattalin arziki. EMT ta ƙunshi jami’ai kamar:

(1) Ministan Tattalin Arziki da Ministan Kudi (EMT Chairman)
(2) Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
(3) Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki
(4) Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari
(5) Ministan Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arziki na Dijital
(6) Ministan Ayyuka
(7) Ministan Kwadago da Aiki
(8) Ministan Noma da Tsaron Abinci
(9) Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur
(10) Ƙaramin Ministan Gas
(11) Ministan wutar lantarki
(12) Ministan Sufuri
(13) Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya
(14) Ministan Ruwa da Tattalin Arziki

Shugaban EMT na iya, kamar yadda ake buƙata, ya kira kowane Ministan Tarayya ko Shugaban Hukumar don yi wa EMT bayani kan muhimman shirye-shirye da ci gaban da suka shafi tattalin arziki.

Ƙirƙirar kafa PECC da Shugaban Ƙasa ya yi a ƙarƙashin shugabancinsa, tare da ƙirƙirar EET, wanda shugaban EMT ya jagoranta, da kuma EMT kanta, alama ce ta haɗaɗɗiyar dabarun da ke nufin inganta tsarin tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya don inganta ƙasar.