Kisan Okuama: Basaraken da ake nema ruwa a jallo ya miƙa kansa

*Sojoji sun tabbatar ‘yan sanda sun miƙa shi gare su

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta ta miƙa Basaraken da aka nema ruwa a jallo, Clement Ikolo Ogenerukeywe, ga sojoji.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Bright Edafe, shi ne ya tabbatar da hakan.

Ana zargin Sarkin Masarautar Ewu ɗin ne da hannu a kisan sojoji 17 da ya auku kwanan nan a jihar ta Delta.

MANHAJA ta naƙalto Ogenerukeywe ya miƙa kansa ne bayan da Babban Ofishin Tsaro ya fitar da sanarwar ya nemansa ruwa a jallo a ranar Alhamis, kamar yadda Kwamishin ‘Yan Sandan Jihar, Abaniwonda Olufemi, ya bayyana.

Bayanai sun ce Basaraken ya isa Hedikwatar ‘Yan Sandan Jihar ne da misalin ƙarfe 6 na yamma.

A wata hira da aka yi da shi a tashar TVC gabanin miƙa kansa, Sarkin ya ce ba shi da hannu kisan sojoji 17 da aka yi a yankin Okuama da ke jihar.

Daga nan, ya yi kira da a zurfafa bincike don bankɗo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.