Hukumar Zakka da Waƙafi ta karɓi Naira miliyan 12 a matsayin zakka a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Naira miliyan 12 ne ke a asusun Hukumar Zakka da Waƙafi da mawadata suka bayar a matsayin zakka a jihar Katsina.

Shugaban hukumar a jihar Dr Ahmed Musa Filin Samji ya faɗi haka a wata hira da ya yi da manema labarai a Katsina.

Ya ce cikin kuɗin Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya bada zakka mafi tsoka ta Naira miliyan goma.

Dr Ahmed Filin Samji ya kuma bayyana cewa hukumar na nan na tantance waɗanda za su amfana da zakka a cikinsu kamar yadda ya ce sun haɗa da nakasassu da ‘yan gudun hijira da kuma waɗanda suka karɓi addinin Musulunci.

Shugaban hukumar sai ya yi kira ga masu hali a jihar da su bada tasu zakkar ga hukumar domin raba wa mabuƙata.

Ya ce zakka ne kawai mafita da zai fidda al’umma daga tsadar rayuwa da halin yanayin tsaro da ake fama da shi a faɗin jihar.

Shugaban hukumar ya ce bada zakka da Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi ya buɗe ƙofa ga masu hali a jihar da suma su zo su bada tasu.