Duk da taɓarɓarewar tattalin arziki, CBN ya ƙara kuɗin ruwa da kashi 24.75

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya ya ɗaga darajar manufofin hada-hadar kuɗi da aka fi sani da ‘kuɗin ruwa’ da kashi 200 cikin 100 zuwa kashi 24.75 daga kashi 22.75 cikin 100 a ƙoƙarin da ake na magance hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamnan babban bankin ƙasar CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen taron manema labarai na kwamitin kula da harkokin kuɗi karo na 294 a Abuja.

Sabon kuɗin ruwa shi ne  kashi 2% daga kashi 22.75 cikin dari da MPC ta sanar kusan wata daya da ya gabata da kuma hauhawar farashi na biyu na kwamitin na yanzu.

Shugaban bankin ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa an daidaita hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar wanda ya kai kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairu.

Cardoso ya ce yanke shawara ne mai tsauri da aka yanke amma akwai yarjejeniya da kwamitin ya yi don ci gaba.