Babu batun rage farashin fetur da gas, inji NNPC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa ya cewa ya rage farashin man fetur da iskar gas.

NNPCL ya mayar da martanin ne kan wasu rahotanni da wasu kafafen watsa labaran Nijeriya ke yaɗawa cewar ya rage farashin man fetur da gas.

Babban jami’in sadarwa na kamfanin Olufemi Soneye ne ya yi watsi da jita-jitar a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai.

Ya kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin.

Sanarwar ta ce, “Kamfanin NNPCL na so ya yi wa al’umma ƙarin haske kan wasu rahotannin da ke cewa ya rage farashin man fetur da gas a cibiyoyin sayar da su.

“Kamfanin na son sanar da jama’a cewa waɗannan rahotanni ba gaskiya bane, sannan yana buƙatar ‘yan Nijeriya su yi watsi da su.

“Tun lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023 farashin litar man fetur ya tashi daga Naira 190 zuwa kusan Naira 700 a Nijeriya.

Lamarin da ya jefa ‘yan ƙasa cikin tsadar rayuwa tare da kiraye-kiraye ga gwamnati na ko dai ta mayar da tallafin ko kuma ta samar da tallafin da zai rage wa al’umma raɗaɗi.