Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shahararren malamin addinin Musluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijeriya sun gayyace shi ya amsa wasu tambayoyi cikin girmamawa.

Duk da cewa, Sheikh bai bayyana waɗanne ɓangare na jami’an tsaron ba ne suka gayyace shi, ya tabbatar da cewa an gayyace shi sun tattauna cikin mutunci da sanin ya kamata.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Ministan Labarai na Nijeriya Mohammed Idris ya bayyana cewa babu wanda ke gaba da doka sai dai wanda bai yi laifi ba.

“Gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wurin samun bayanan da za su magance mana matsalarmu.

“Jami’an tsaro suna tsaya kyam, Gumi kamar kowane ɗan Nijeriya yake, bai wuce doka ba.

“Idan yana da shawarwarin da ya kamata jami’an tsaro su ɗauka sai ya ba su su ɗauka.”

Sai dai a nasa vangaren , Dokta Gumi ya ce, “babu wani dalilin fargaba.
Ya wallafa hakan ne a shafinsa na sada zumunta yana mai cewa, “mutum ɗaya ne kawai ya fi qarfin doka: shi ne wanda bai yi laifin komai ba!”

Ya ce, “A daren jiya na samu kiraye-kiraye da yawa daga masoya da makusanta da ‘yan jarida kan wani labari na cewa jami’an tsaro sun gayyace ni sun yi min tambayoyi.

“Babu shakka an yi haka, amma babu dalilin ɗaga hankali.

“Tabbas, mun samu kyakkyawar fahimta mun kuma tattauna kan yadda za a daƙile ayyukan ta’addanci.

“Babu cin mutuncin da ya shiga tsakanina da su sai ma karamci da girmamawa.

“A matsayinmu na al’umma dole mu haɗa kai mu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

“Na gode da kulawarku. Allah ya ci gaba da tsare mu daga dukkan sharri. Amin.”