Birtaniya ta haramta wa likitoci ‘yan Nijeriya masu aiki a ƙasar zuwa da ‘yan uwansu

Daga BASHIR ISAH

Ƙasar Birtaniya ta haramta wa ma’aikatan kiwon lafiya a ƙasar zuwa da ‘yan uwansu ƙasar.

Ofishin cikin gida na Birtaniya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne a matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnatin ƙasar ke yi wajen yaƙi da matsalar shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Ta ƙara da cewa a bara kaɗai, jimillar ma’aikata 120,000 ne suka raka ma’aikata 100,000 zuwa Birtaniya.

“Masu ba da kulawa a Ingila da ke aiki a matsayin masu tallafawa bakin haure kuwa, za a buƙaci su yi rajista tare da Hukumar Kula da Lafiya (CQC) – mai kula da masana’antu don Kiwon Lafiya don murƙushe cin zarafin ma’aikata.

“Hakan ɓangare ne na ƙwararn matakan da aka ɗauka wanda za a aiwatar ba da daɗewa ba, wanda ke nufin adadin mutane 300,000 da suka cancanci zuwa Birtaniya a bara ba za su iya yin hakan ba.”

An ambato Sakataren cikin gida, James Cleverly MP, yana cewa: “Ma’aikatan kulawa suna ba da gudummawa ainun ga al’ummarmu, suna kula da ‘yan uwanmu a lokutan buƙata.

“Amma ba za mu iya ba da hujjar rashin aiki ba ta fuskar cin zarafi, maguɗin tsarin shige da ficenmu da adadin masu ƙaura marasa dorewa.