Ƙarancin Abinci: Gwamnan Kano ya yi kira kan a sake buɗe iyakokin ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka ya sake buɗe iyakokin ƙasa don shigowa da kayan abinci wanda a cewarsa, hakan zai taimaka wajen daƙile ƙarancin abincin da ake fama da shi a ƙasa.

Wannan kira na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wadda aka fitar jim kaɗan bayan da Gwamnan ya karɓi baƙuncin Kwantrola Janar na Hukumar Fasa-ƙwauri ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, a Fadarr Gwamnatin Jihar da ke Kano.

Gwamna Yusuf ya koka kan yunwar da ake fuskanta a ƙasa wanda hauhwar farashin kayayyaki ya haifar.

Ya ce, “Muna godiya da yaba shirin ba da tallafin abinci na Shugaban Ƙasa da ke gudana wanda aka ayyana Kano a matsayin wurin da za a ƙaddamar da shirin.

“Muna da yaƙinin shirin zai taimaka wajen rage raɗaɗin ƙarancin abincin da ake fama da shi muddin aka aiwatar da shi.”

Abba ya ƙara da cewa, wani makin har wa yau da zai yi tasiri wajen magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasa shi ne, Gwamnatin Tarayya ta sake buɗe iyakokin ƙasa domin a shigo da kayan abinci.

Yayin ganawarsu, Gwamna Abba ya jaddada wahalar da ‘yan ƙasa ke fuskanta sakamakon ƙarancin abinci musamman a watan Ramadan.

Kazalika, Gwamnan ya yaba wa hukumar ta Kwastom bisa shirinta na raba kayan abinci ga wasu jama’ar Kano don rage musu raɗaɗin rayuwa.