Kin iya kunu?

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku mai albarka na zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A makon da ya gabata mun yi batutuwa masu muhimmanci a game da aure da mu’amalar aure. A wannan mako kuma masu karatu mun kawo muku tsaraba daga madafi, musamman ma duba da ƙaratowar qatan azumi. Muna fatan Allah ya raya mu zuwa lokacin. A sha karatu lafiya.

Kin iya kunu? Waɗannan kalmomi wasu kalmomi ne da suka yi shuhra a watannin baya a dandalin sada zumunta. Kodayake abu ne da ya zo kamar a zolaya aka dinga yaɗawa har wasu suka dinga juya maganar kunun da wata ma’ana ta daban.

To yanzu dai uwargida ko amarya mu ajiye wasa a gefe, kin iya kunu? Waɗannan kalmomi ba kunu kaɗai nake nufi ba. Abinda nake nufi shi ne, kin san sirrin madafi/kicin/ɗakin girki?

Da farko dai abinda mata da yawa ba su fahimta ba, girki yana da matuƙar muhimmanci fiye da yadda suke tsammani a cikin gidan aure. Kuma rashin iya girki mai kyau da kula da cimakar mai gida ba ƙaramin gurgunta aure suke yi ba. Mata da dama suna ganin idan sun yi wa miji kwalliya, sun gamsar da shimfiɗarsa sun gama komai. Amma gwana a cikin mata wacce za ki ga ta zama ‘yar gaban goshi to wallahi ki bincike ta za ki ga ta san sirrin tukunyarta.

Kuma ba wai girkin miji kaɗai ba, har ma na yara da kuma ki san yadda za ki yi ki tafiyar da harkar madafin. Ga wasu hanyoyin na sanin makamar aiki ga iyayen gida da amare wanda matuƙar sun kiyaye su, ko’ina za a je suna da ƙwarin gwuiwar amsa tambayar sun iya kunu da eh!

  • Kalar abincin da ake so: Da farko kafin a je batun kin iya ko ba ki iya ba, ki fara gano wanne ma kalar abinci yake so? Komai iyawarki in dai ba kalar da yake so kika iya ba, to kin faɗi jarrabawa. Wasu mazan sun fi son tuwo, da za ki yi musu kowanne irin girki ne matuqar ba tuwon nan ba ko abincin gargajiya ba ba za ki birge su ba.

Wani kuma ya fi son abinci irin na zamani. Kayan gargajiya ba su dame shi ba sam-sam wannan ma yana da matuƙar muhimmanci ki san ina ma ya fi karkata a kai sai ki dage a wannnan ɓangaren. Domin farin cikinsa kike nema, kuma wannan farin cikin kaɗai zai iya kai ki ga rahamar Allah.

  • Lalura: Abu na biyu shi ne, laura. Ki kula da lalurar mijinki. Saboda ke ce mai ba shi abinci. Akwai wasu rashin lafiyar da sauƙi ko tsananin lalurar yana da alaƙa ta ƙus da ƙus da abinda suke ci. Mu duba rashin lafiya kamar ciwon suga, hawan jini, ciwon hanta, gyambon ciki (Ulcer) da makamantansu. Dukka waɗannan lalurori da na lissafa fa lalurori ne masu haɗari da suke buƙatar kulawar abinci.

Ke kuma a matsayinki na mai ba shi abinci kin ga sauƙi da warakarsa da tsanantar ciwonsa gabaɗaya ma yana a hannunki kenan. Don haka, sai ki kiyaye da kyau. Idan ciwon suga ne sai a kiyaye ɓangaren sukari, da abinci nau’in carbonhydrates da za su iya ta’azzara ciwon nasa. Ki nemi shawara wajen masana tare da bincike. Yanzu zamani ne na intanet komai ya zo da sa sauƙi kina lalubowa za ki samu amsa.

Amma ki dage da ɓangaren sarrafa alkama ta yin dashishi, alkubus, funkaso, ɗanwaken alkama, dambun alkama ko na acca, kunun alkama ko na acca, faten acca, tuwon alkama ko na dawa, haɗin salak da sauransu. Har na zamani ma za ki iya yi idan kin bincika ba illa.

Sanann mai hawan jini a rage gishiri da magi a girki a fi yi masa amfani da kayan marmari masu launi da sauransu. Idan gyambon ciki ne, a kiyayi cika yaji da mai a girki. Kuma a dinga yi masa abinci a kan kari kada ya cutu. Idan so samu ne kuma ma a dinga yi masa girki yana tafiya da shi aiki saboda masu lalura suna wahalar samun abinda za su ci wanda ya dace da lafiyarsu a waje.

  • Lokacin abincinsa: Abu na uku, a kula da lokacin cin abincinsa. Kamar yadda na faɗa a sama, musamman masu lalura. Musamman masu ciwon suga da gyambon ciki (Ulcer) suna matuƙar buƙatar a dinga yi musu abinci a kan kari. Abincin karin kumallo da wuri ake son su dinga ci. Ko da ba shi da lalura don Allah a daina bari lokacin dawowarsa ya yi ba tare da an kammala masa girkinsa ba. Yana fusata maza hakan sosai.

*Tsafta: Ya kamata uwar gida ta dinga tsaftace wa maigida abincinsa da mazuban abinci. Har ma da muhalli. Ko don lafiyarta da ta iyali. Ba daɗi kina girki a kicin kina tsifa ko wani abu da bai dace ba. Ko ki bari ƙura ko wani abu ya shiga girkin. Shi ya sa wani zubin sai a ga gashi ko wani abu a cikin abinci. Ki kula sosai. Sannan kwanukan abincin miji ki ware su daban, sannan ki dinga wanke su da kyau.

Banda tsoma ‘food flask’ a ruwan wanke-wanke, a ɗauraye shi a waje ya fi daxewa bai lalace ba. Sannan a dinga wanke shi da soson katifa maimakon soson wanke-wanke, hakan zai sa zane ko ƙyallin jikinsa ya daɗe bai goge ba. Sannan wajen wanke-wanken a dinga farawa da kofuna saboda kada su shafu da maiƙo. Idan so samu ne ma kada a cakuɗa kofuna da komai a wajen wanki.

A nan za mu dakata. Da yardar Allah mai kowa mai komai za mu ci gaba a mako mai zuwa. Allah ya sada mu da alkhairi. 08024859793.

By Editor