Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU) da ta NASU sun fara yajin aikin gargaɗi na mako guda don neman a biya su albashinsu na wata huɗu da ya maƙale bayan yajin aikin gama-gari a 2022.
Ƙungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniyar shiga yajin aikin ne bayan taron da suka yi a Akure a ƙarshen makon da ya gabata.
Yayin da yake karanta wa manema labarai sakamakon taronsu ran Litinin a Abuja, Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya ce sun yanke shiga yajin aikin bayan ƙure amfani da hanyoyin da suka dace ba tare da cimma buƙatarsu ba.
“Idan Gwamnatin Tarayya ta gagara ɗaukar matakin biya mana buƙatarmu, ƙungiyoyin biyu za su sake haɗu don ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan batun,” in ji sanarwar.
Duk da dai Shugaba Bola Tinubu ya ba odar a biya ma’aikatan jami’o’i albashinsu da aka riƙe sakamakon yajin aiki a 2022, sai dai ƙungiyoyin SSANU, NASU da kuma NAAT sun ce har yanzu ba su gani a ƙasa ba, kuma ta bada gargaɗi na mako guda a makonnin da suka gabata.
A hirarsu da tashar Channels Television a ranar Lahadi, shugaban SSANU ya yi zargin Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da su.
