Lawal ya jagoranci taron Majalisar Zatarwa, ya buƙaci mambobi su yi aiki da gaskiya

Daga BASHIR ISAH

A zaman Majalisar Zartarwar jihar da ya jagoranta a ranar Litinin, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi kira ga mambobin majalisar da su yi aiki da gaskiya tare da sauke nauyin da rataya a wuyansu yadda ya kamata.

Taron ya gudana ne a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta ce majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da dama yayin zaman da suka haɗa da ƙudirin ciyar da jihar gaba, kiwon lafiya, batun ilimi, tsaro da sauransu.

A cewar sanrwar, wannan shi ne karo na takwas da majalisar ke zamanta tun bayan da Lawal ya kama mulki.

Yayin taron, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cimma nasarar bunƙasa jihar.

Daga nan, ya ƙarfafa wa mambobin majalisar kan su mutunta nauyin da ke kan kowannensu.

Bugu da ƙari, an yi wa taron bayani kan inda aiki ya kwana dangane da aikin yi wa sakatariyar jihar kwaskwarima da ke gudana.