Ku yi wa Allah ku tallafa wa talakawan ƙasa, roƙon Tinubu ga su Ɗangote

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi hamshaƙan ‘yan kasuwar ƙasar, wato Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da sauran masu ƙumbar susa, da su dubi Allah sannan su taimaka wa marasa galihu musamman a wannan wata na Ramadan.

Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Lahadi a Kano a wajen ƙaddamar da shinkafar da Santa Abdullahi Yari ya tanada don tallafa wa jama’a don girmamawa ga Shugaba Tinubu.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa kuma hadiminsa, Abdulaziz Abdulaziz, inda ya yaba da karamcin da sanatan ya nuna masa.

Ya ce an ƙaddamar da tallafin ne domin tallafa wa waɗanda ke cikin tsananin buƙata.

A cewarsa, “Harkar shugabanci ba na mutum guda ba ne, kuma haka lamarin yake duk duniya. Akwai buƙatar a taimaka wa mabuƙata a cikin al’umma.

“Mu haɗa hannu sannan mu dunƙule a matsayin ƙasa ɗaya don cigaban ƙasa,” in ji shi.

Tinubu ya yaba wa Yari bisa tallafin da ya bayar na manyan motoci 140 maƙare da shinkafa don amfanin marasa galihu.

Daga nan, Tinubu ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen yi wa ƙasa addu’a da samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Da yake jawabi tun farko, wakilin Yari, Dr Abubakar Danburam, ya ce motoci 140 ɗin na ɗauke ne da buhun shinkafa 84,000 masu nauyin kilohitam 50.