Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Barka da safiya malama Aisha. Na san ba ki san ko wacce ce ni ba, sunana…………kuma na samu number ki ta hannun Hajiya…………ƙawata ce, lokacin da na ke mata bayanin halin da nake ciki ne, sai ta ce, ga number na kira ki, ke ce wadda ki ka zo har gida lokacin da matsalarta da……………..ta yi tsanani, ke ki ka taimaka har aka samu mafita.

Malama Aisha, mijina ne can baya shekaru da yawa, shi da wani wan babanshi suka shigo da yamma, wan baban nasa ɗauke da jinjiri, suka ce a Masallacin unguwar wan baban ne aka ajiye shi, ba a san waye ya ajiye ba. Shi ne wan baban ya ba wa mijina shawarar me zai hana ya ɗauka ya riƙe tunda mu ba mu sami haihuwa ba. Shi ne mijin nawa ya ce sai dai idan na aminta da hakan. Na karɓi yaron na riqe, shi kuma maigidana ya siyo duk abinda ya kamata muka kula da jinjirin.

Shekaru biyu bayan nan na samu haihuwa ni ma dai namiji. Na haɗa su su biyu. Ban tava nuna bambanci a tsakanin su ba. Shekaru huɗu bayan haka, maigidana ya ƙara dawowa tare da limamin unguwarmu tun da asubahin, limamin na san shi sosai don shi ke wa’azi duk bayan magariba zuwa Isha’i.

Hannunshi ɗauke da wani jinjiri, wai an ajiye shi a Masallaci kafin a yi kira, ko da ya shigo ya same shi a ciki. Shi ne ya nemi maigidana tunda ya ji labarin yadda ya yi aikin Allah a wancan karo, ko za mu ƙara da wannan. Anan ya dinga yi min wa’azi da nunamin falalar renon jinjirin, har sai da na ji jikina ya yi sanyi, na amince na karɓe shi matsayin ɗana na uku.

Yanzu yaran sun girma, sai kuma ‘yan surutai suka fara tashi na kamar da yaran ke yi da juna, kuma wai suna kama da maigidana, tun ina musanta abin, har zuciyata ta fara yi min kwashe-kwashe, har ni ma na fara hango kamar.

Ds abin ya yi yawa ne, sai na fara tunanin fitar da kaina daga tunanin. Ranar muna kwance a ɗaki, na cewa maigidana, ɗazu mun yi baƙi da bayanan, kamar na kira shi a waya, tsabar ruɗewa ya sa ban kira ba. Na ce masa wata mata ce da mijinta suka zo wai babban yaron, sunansa…………….ɗansu ne. wallahi malama Aisha sai kinga yadda ya ruɗe, ya tashi cikin firgici, bai tsaya jin komai ba ya dinga ƙaryata su. Ya sa kayanshi ya fice daga gidan, bai dawo ba sai 12.

Akan wannan maganar sai da aka yi wata bai dawo hayyacinsa ba. Kullum zancen ɗaya ne, hakan sai ya ƙara min zarginsa. Ki ba ni shawarar yadda zan bi da lamarin, ta yadda ba zan yi nadama ba. {Saƙon ya zo ta murya ne, don haka yi tsayi sosai, hakan ya sa dole muka katse wasu batutuwa}.

AMSA:

Tun daga farko zan so mu fara da falala, girma da ladan da ke cikin riƙe ɗan da yake maraya ko wanda aka yada ba shi da kowa. Yayin da ki ka bi bayanan malamai kan irin ladar da ki ka samu a riƙon da ki ka yi, za ki amince da cewa, duk yadda lamarin ya kasance wallahi kin ci riba, domin ba xan qaramin aiki za a yi ba a cimmaki wurin lada.

Abu na biyu, idan na fahimce ki sosai kina so ne ki samu hanyar warware matsalar ba tare da kin tunkari mijinki ba, don gudun zaman zargin naki ba gaskiya, wanda hakan zai iya buga guduma a auren ku, wadda abin rufe ta zai yi wahala.

Wanna ɗabi’a abu ce da ya kamata mata su yi koyi da ita, ba wai na ce tunkarar miji da wasiwasin da ku ke samu kansu laifi ne ba, sai dai rashin sanin irin zargin da ya kamata ku tunkari mazajenku da su ne matsalar.

Idan mace ta zargi mijinta da daina sonta, saboda wasu alamu da take gani, wannan ba laifi ba ne faɗa masa kai tsaye da kuma makamantansu da ba su taka kara sun karya ba. Amma zargi kamar irin na zina ko sata da sauransu furtasu ba tare da wata ƙwaƙwarar hujja ba matsala ce babba ga aure, sai dai ba yana nufin ki bar abin ya yi ta cin ki a rai ba, har ya haifar da wata rashin jituna da miji bai san asalinta ba. Domin shi zargi tamkar shuka ne, girma yake yi idan ba a kawar da shi ba, idan kuwa ya girma, yana haifar da ƙiyayya ta babu dalili.

Anan abin nufi dai shi ne, kafin ki zargi mijinki da aikata wani babban laifi, zai fi kyau a ce kin samu hujjar da ta wuce yaye-yayen zuciya ko surutun mutane. Sai dai idan kin yi iya yinki ne ba ki samu ba, wannan kuwa tunkarar sa ne ya fi alheri fie da ki yi ta zama da abin a ranki.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.