Domin ku matan aure

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar al’umma Manhaja, sannunku da jimirin bibiyar mu.

Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo ma ku wasu daga ci gaban kayan da za su samar da ni’ima dawamamma ga mace, kuma kayan da ta ke da tabbacin tsafta da lafiyar su, kasancewar ita da kanta ne zata dinga haɗawa. Sai dai kafin nan, zan so in yi amfani da wannan dama in janyo hankalin mata kan illar shan maganin mata da ke bayar da ni’ima ta ɗai rana.

Mata ku guji amfani da maganin mata mai bayar da ni’imar ɗai-rana, na san da yawa za su ga zancen tamkar maganar son rai, sai dai zan yi amfani da misali mafi sauƙin ganewa.

Ke ce ki ke da ɗa, wanda a kullum kina ba shi kunu ba tare da sukari ba, wannan shi ne abinda ya saba da shi, don haka da ya ji yunwa, cikin shauƙi zai karɓi kunun yana sha, daɗin ɗanɗanon geron na ratsa bakinshi. Me ya sa yake son kunun a haka? Saboda ɗanɗanon da ya sani kenan, kasancewar shi kaɗai ki ka saba masa da shi.

Sai kwatsam a wata rana, ki ka siyo sukari mai yawa, ki ka malala a kunun, ya yi zaƙi matuƙa, ki ka ba shi ya sha, shin ya makomar zata kasance idan ki ka yi ƙoƙarin ba shi kunun gobe ba sugan? Ina ga ko ya karɓa, zai sha ne a rashin so, ba don yana so ba, sai don tsoron da yake ma ki ko yunwar da yake ji.

Idan kina so ya cigaba da shan kunun yadda ya saba, to dole sai idan kullum za ki siyo adadin wannan sukari ki zuba masa a kunun, wanda hakan zai iya zama illa, saboda nacewa abinda idan ya yi yawa zai iya cutarwa.

A ɓangare ɗaya, misalin wadda ta ke amfani da kayan da za su bata ni’ima dawamamma shi ne, misalin wadda ta siyo suga mai yawa, sai dai a kullum zata sanya haɗan a kunun, kuma zai wadatar da mai sha, kasancewar zai ji ƙari ne fiye da jiya, wannan zai sa ya dinga marmarin kunun, saboda kullum ta fi jiya zaqin, har a kai lokacin da zaƙin zai yi yawa sosai, kuma ya tsaya a hakan ba tare da an koma baya ba (sai idan kin ɗauki wasu ɗabi’u da muka faɗa a baya suna disashe ni’ima).

Idan mun koma kan darasin namu, zan fara da matan da ke fama da matsala ta buɗewa, wataƙila ta sanadiyyar haihuwa, ɗaukar abu mai nauyi, aikin wahala da makamantan su. Za su iya neman garahuni garin shi, miski fari, garin ceɗiya da kuma man kaɗanya. Za ku kwava su wuri ɗaya, su haɗe sosai, sai a yi matsi da shi tsayin awanni uku, sannan a wanke da ruwan ɗumi.

Har wa yau, ana samun ganyen zogala, garin kanunfari, minanas, zuma da garin habbatu sauda, a haɗe su, a yi matsi, awa biyar kafin a wanke.

Kuma an tabbatar da cewa, haɗin bagaruwa, zuma, kanunfari ba iya kawar da ciwon sanyin mata yake yi ba, yana matse mace, musamman idan ruwan da aka wanke shi dafafen ruwan hulba ne.