Aiwatar da Rahoton Oronsaye zai rage wa gwamnati kashe kuxi – RMAFC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tarawa da Raba Kuɗin Shiga (RMAFC), ta yi ƙorafi kan maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnati.

A baynin da ta fitar a ranar  Lahadi, RMAFC ta ce salon mulki mai tsada da da rashawa da sauransu na daga cikin dalilan da kan  haifar da kashe kuɗi mai yawa wajen gudanar da harkokin gwamnati.

Don haka hukumar ta ce, tana da yaqinin kan cewa aiwatar da Rahoton Kwamitin Steve Oronsanye wanda Majalisar Zartarwa amince da shi kwanan nan, zai taimaka matuƙa wajen daidaita tattalin arzikin ƙasa da kuma kyautata rayuwar ’yan ƙasa.

Shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu, shi ne ya  bayyana haka a Abuja.

Ya ce hukumar ta lura cewa, yawan kashe kuɗaɗen da gwamnati kan yi shi ne ummul aba’isin gazawar gwamnati wajen samar abubuwan morewa rayuwa da da kyautata rayuwar ‘yan ƙasa yadda ya kamata.

Ta lura cewa “babu al’ummar da za ta cigaba dole sai ta samar da ingantaccen tsari na tattali ta yadda za a riƙa sarrafa arzikin ƙasa don kowa ya amfana,” in ji shi.

Ya ce sheka da dama da suka shuɗe, RMAFC ta yi kira da a duba sannan a rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnati a matsayin hanya ta tattalin arzikin ƙasa.