26
Feb
Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu ƙwararriyar marubuciya ce da ta daɗe tana jan zaren ta a duniyar rubuta littattafan Hausa. Kuma ta yi zarrar zuwa ta biyu a gasar da sashen Hausa na BBC ke shirya wa mata zalla a duk shekara, wato ‘Hikayata,’ a shekarar 2019. A wannan tattaunawar da wakiliyar Manhaja, za ku ji yadda marubuciyar ta sha gwagwarmaya da faɗi-tashi a harkar rubutu. Daga AISHA ASS Mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.Bismillahir Rahmanir Rahim! Suna na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu. An haife ni a shekara ta 1980. Na yi karatu tun daga firamare zuwa Jami’ar Bayero…