Henna Ball da People’s Award na 2026: Gidan talabijin na Tozali zai yi taron dawo da karsashin matan da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidan talabijin na Tozali na farin cikin sanar da al’umma cewa zai gudanar da taron bayar da lambar yabo na Henna Ball da Tozali People na 2026.

Za a gudanar da taron ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2026 a ɗakin taro na Los Angeles, inda za a martaba ƙoƙari, al’ada, jajircewa da tasirin ayyukan jin-ƙai acikin al’umma.

Haka kuma, an yi wa taron laƙabi da Empowering Survivors. Restoring Hope.”, wato mai manufar inganta rayuwar matan da suka shaƙi iskar ‘yanci bayan garkuwa da su da kuma dawo da karsashinsu acikin al’umma.

Sannan, taron zai tara sanannun mutane ciki har da jagororin gwamnati, ‘yan kasuwa, masu ƙirƙira, masu nishaɗantarwa, masu taimakon al’umma, jagororin al’umma da kuma masu muradin kawo sauyi domin taya waɗanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen yin ababen yabo a Nijeriya.

An tsara wannan taro ne da nufin karrama mutane da ƙungiyoyin da suka yi nasara ta fuskar aiki tuƙuru da sadaukarwa, jajircewa da juriya, sauyi mai kyau da ya yi tasiri acikin al’umma, baiwa da ƙwarewa ta hanyar nuna wa duniya fitattun mutane a Nijeriya da ke ƙoƙarin samar da sauyi a yankunansu.

Akan haka ne Tozali TV ya gayyaci ƙungiyoyi, cibiyoyi, da mutanen da ke hangen inganta yankuna da samar da ci-gaba domin haɗa hannu da Henna Ball da Tozali People’s Award 2026.

Domin ƙarin bayani, za a iya tuntuɓar Fatima Isa, wato jami’ar shirya taron ta lamba kamar haka: +234 816 051 6053, ko kuma adireshin Imel: [email protected]

By Babaji

Leave a Reply