30
May
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙalubalanci masu ruwa da tsaki da duka mambobin jam’iyyarsu ta APC maici a yankin Arewa ta tsakiya a ƙasar nan su tabbatar sun ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Wannan kiran haɗin kai Shugaban Ƙasar ya yi ne a lokacin wani gagarumin taron masu ruwa-da-tsakin jam’iyyar APC ɗin a Arewa ta tsakiya wanda aka gudanar a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar Nasarawa. Shugaba Tinubu wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya wakilce shi a wajen taron, ya jaddada mahimmancin haɗin kai don cigaban jam’iyyar ta APC da ma ƙasa baki ɗaya. Ya…
