28
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Fafutukar Yaƙi da Cin Hanci a Nijeriya, SERAP, ta kai ƙarar gwamnonin jihohin ƙasar 36 da Ministan Birnin Tarayya, Abuja, saboda zarginsu da gaza yin bayanin yadda suka kashe maqudan kuɗaɗen da suka samu daga kason Asusun Tarayya na FAAC, tun daga shekarar 1999. Cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare ya fitar ranar Lahadi, ya ce qungiyar ta ɗauki matakin ne sakamakon rahoton da ta samu cewa a cikin watan Maris FAAC ta raba Naira Tiriliyan 1.123 tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi. Ƙunhiyar ta ce, haka…
