Editor

9416 Posts
Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta rufe babban ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos Electricity Distribution Company (JEDC) a Jihar Filato kan ƙarin kuɗin wuta. Binciken Manhaja ya gano NLC ta rufe babbar ƙofar shiga kamfanin lamarin da ya haifar wa ma'aikatan DisCo tsaiko wajen shiga ofishin. Kazalika, NLC ta girgiza kamfani rarraba wutar lantarki na Yola Electricity Distribution Company (YEDC) a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba duk dai kan batun ƙarin kuɗin wuta. Dukkan wannan ya faru ne a ranar Litinin a ci gaba da gwagwarmayar da NLC ke yi wajen tabbatar da 'yan ƙasa…
Read More
Za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohi N724bn a 2024

Za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohi N724bn a 2024

Daga BASHIR ISAH Majalisun tarayya da na jihohi 36 a Nijeriya za su kashe kimanin Naira biliyan 724 wajen gudanar da harkokinsu a 2024 da ake ciki. Bayanai kan yanayin kuɗaɗen da za a kashe wa 'yan majalisun tarayya da na jihohin a wannan shekarar sun ce, a ɓangare albashi da alawus-alawus kaɗai kimanin Naira biliyan 50 aka ware a kasafin ƙasa. Sannan biliyan N673.94 wajen sauran harkokin majalisun na tarayya da jihohi da kuma hukumomin da ke ɗamfare da su. Yayin da za kashe biliyan N8.67 wajen biyan albashi da alawus-alawus na 'yan majalisa 109 a matakin tarayya, a…
Read More
Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da aiwatar da harajin rabin kashi ɗaya (0.5%) na tsaron internet wanda ya tada ƙura a ƙasa, tare da neman a sake nazarin dokar. Idan ba a manta ba a ranar 6 ga Mayu, CBN ya fitar da sanarwa tare da umuryar bankuna da su ɗabbaƙa sabon haraji na tsaron intanet. Sabuwar dokar ta nuna za a riƙa biyan kashi 0.5 na hada-hadar kuɗaɗe ta intanet sannan a tattara a zuba a asusun Taaron Intanet ƙarƙashin kulawar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara…
Read More
Inuwa zafi, rana ƙuna

Inuwa zafi, rana ƙuna

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A lokacin da a ke tsananin zafi mutane kan nemi ruwa mai sanyi ko wajen mai inuwa don rage kaifin ƙalubalen yanayin. A wasu shekaru ma da idan wasu bai gama wayewa ba su kan ɗora ƙanƙara a kansu su kifa hula har ta kai ga an samu matsalar daskarewar jini da kan iya haifar da asarar rai. Abun da na ke son magana a kai wannan makon shi ne yadda tsananin zafin rana kan ƙare a kan talakawa wajen neman abinci amma ba lallai ne su samu ba don yadda rayuwa a zamanin yau…
Read More
Babban likitan Falasɗinu ya rasu a kurkukun Isra’ila

Babban likitan Falasɗinu ya rasu a kurkukun Isra’ila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyoyin masu kula da fursunonin Falasɗinu sun ce wani babban likita Bafalasɗine ya mutu a gidan yarin Isra'ila bayan shafe sama da watanni huɗu yana tsare. Dr Adnan Al-Bursh, mai shekaru 50, shi ne shugaban likitoci a asibitin al-Shifa. Ma'aikatar gidan yarin Isra'ila ta tabbatar da cewa wata sanarwa da aka buga a ranar 19 ga Afrilu game da wani fursuna da aka tsare saboda dalilan tsaron ƙasa ya mutu a gidan yarin Ofer shine Dr Al-Bursh. Ba a bayar da cikakken bayani kan musabbabin mutuwar ba, kuma hukumar gidan yarin ta ce ana binciken lamarin.…
Read More
Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Jimoh Ibrahim

Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Jimoh Ibrahim

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yawancin ministocin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ba sa ƙoƙari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a Jam’iyyar APC. Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu kuma ba sa tavuka komai. Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels. A cewar ɗan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin ƙasar, amma babu wani tsari da mataimaka da za su sa ga kai gaci.…
Read More
Jami’in KEDCO ya kashe abokin aikinsa a Kano

Jami’in KEDCO ya kashe abokin aikinsa a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana ɓacewar Bello Bukar Adamu, wani mazaunin Kano kuma jami’in Kamfanin Lantarki na Kano (KEDCO), bayan ya samu kiran gaggawa daga Sadik, matashin da ake kyautata zaton amininsa ne kuma abokin aikinsa a Kamfanin na Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO. Bayan kwana biyu ne kuma a ka tsinci gawar tasa a wani titi da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar. Abdullahi Abubakar, ƙanin Bello, ya ce marigayin yana a gida da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, lokacin da Sadiq ya yi masa kira na gaggawa. Ya ce suna…
Read More
Editan FirstNews ya aijiye aikinsa bayan tsare shi da sojoji suka yi

Editan FirstNews ya aijiye aikinsa bayan tsare shi da sojoji suka yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Editan FirstNews, Segun Olatunji, ya yi murabus sa’o’i bayan da jaridar ta nemi afuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila. Olatunji, wanda ya shafe kwanaki 14 a hannun hukumar leƙen asiri ta tsaro (DIA) da ke Abuja domin bayar da rahoto kan Gbajabiamila, ya ce ya yi murabus ne domin kare lafiyarsa da na iyalansa. Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da Olatunji ya rubuta mai taken: “Yadda Gbajabiamila ya yi yunqurin karkatar da dala biliyan 30, gidaje 66 ta hanyar Sabiu”. Kamfanin FirstNews, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 8 ga Mayu,…
Read More
Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya rasa ɗa da ƙani a hatsarin mota

Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya rasa ɗa da ƙani a hatsarin mota

*Yayin da matarsa ta rasa idonta guda Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Tijjani Babangida, ya rasa ɗansa Fadil mai kimanin shekara guda da haihuwa a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su. Haka nan, an ce matarsa Maryam ta rasa idonta ɗaya a sakamakon hatsarin wanda ya auku ranar Alhamis a hanyar Zariya zuwa Kaduna. Kazalika, wani ɗan uwan mahaifin Tijjanin, mai suna Ibrahim Babangida shi ma ya rasu sakamakon hatsarin. Har wa yau, bayanai sun ce wani ƙarnin Tijjani mai suna Ibrahim wanda shi ma yake cikin motar, nan take rai ya yi…
Read More
Gwamnati ta sanar da lokacin da za a kammala hanyar jirgin ƙasan Kano-Daura

Gwamnati ta sanar da lokacin da za a kammala hanyar jirgin ƙasan Kano-Daura

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta ce za a kammala aikin layin dogo na Kano-Daura ya zuwa 2025. Ministan Sufuri, Said Alkali, ya ba da tabbacin hakan ne yayin zantawarsu da manema labarai ranar Juma'a a Abuja bayan ziyarar gani da idon da ya kai inda ayyukan hanyar jirgin ƙasan Kano-Maradi da Kaduna-Kano ke gudana. A cewar Ministan, wannan aikin na daga cikin muhimman ayyukan da Ma'aikatar ke ƙoƙarin ganin ya kammala don a fara cin moriyarsa. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai…
Read More