26
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin injin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwance a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. Jaridar Punch a Nijeriya ta ruwaito cewa an samu gawarwakin mutanen galibinsu ɗaliban Jami'ar Neja Delta a cikin ɗakin Kiɗe-kiɗe watau 'studio' ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin. Jaridar ta ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne. An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauke su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe…
