Yanzu-yanzu: Abba ya ba da umarnin kama tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin gaggawa kan a tsare tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

News Point Nigeria ta rawaito cewar, Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne ya shaida wa manema labarai hakan da safiyar Asabar.

A cewar Yusuf, ‘Komawar Aminu Ado Bayero Kano ba komai ba ne face haddasa rashin lumana a jihar’.

“Don haka na bai wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar umarnin ya kama Alhaji Aminu Ado Bayero, a duk inda ya gan shi a jihar,” in ji sanarwar.

By Editor