Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya wajen yaƙi da ɓarayin daji a faɗin jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci taron majalisar tsaron jihar Zamfara a Fadar Gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.
Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwmanan, Sulaiman Bala Idris, taron ya mai da hankali ne kan sha’anin tsaron jihar da kuma yaƙi da ɓarayin daji da ke gudana a jihar.
Sanarwar ta rawaito Lawal na cewa, “Taron yau zai auna sha’anin tsaron jihar ne don sanin nasarorin da muka samu, da kuma tantance ɓangarorin da ke buƙatar a mai da hankali kan su ainun don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Kamar yadda na sha faɗa wa majalisar tsaro cewa, ɓangare da gwamnatina ta fi mai da hankali shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Don haka, a shirye muke kowane lokaci don ba da goyon baya ga hukumomin tsaro a jiha domin mu tallafa musu wajen gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
“Ina godiya ga Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojojin bisa ƙarin dakarun da aka tura Zamfara. Wannan mataki ne da aka ɗauka don kakkaɓe ɓarayin daji, kuma mu soma ganin sakamakon haka,” in ji Lawal.
