Daga WAKILINMU
A yayin da aka kammala shirye-shiryen buɗe tashar sabon jirgin ƙasan Abuja a ranar 29 ga watan Mayu, Ministan babban birnin, Nyesom Wike, ya shaida wa manema labarai cewa tuni Shugaba Tinubu ya buƙaci da a ɗebi fasinjoji kyauta na tsayin wata biyu a jirgin ba tare da an karɓi ko sisinsu ba.
Hakan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Tarayya ta ce ta sami ragin Dala Milyan 53 a aikin wanda a ka kammala shi a kan kuɗi Dala milyan 75 maimakon Dala milyan 128 da gwamnatin baya ta ce za a yi aikin.
Ministan ya ce, za su yi amfani da wani sashi na rarar kuɗin don samar da wasu ababe da ba a tanadarwa tashoshin jirgin ƙasan ba wanda suka haɗa da na’urorin sanyaya wuri a inda fasinjoji ke dakon jirgi, da samar da matattakalar dattijai da masu buƙata ta musamman da ma kumbon hawa da sauka, wato Lifter a Turance.
Zuwa yanzu, sabon jirgin jigilar na da tashoshi takwas ne da suka haɗa da Abuja Metro, Stadium, Kukwaba I, Kukwaba II, Wupa, Idu, Basanjiwa, sai tasharsa ta filin jirgin sama.
