Tinubu ba zai iya magance matsalolin Nijeriya a shekara ɗaya ba — Sanusi II

Spread the love

Daga WAKILINMU

An bayyana cewa, da kamar wuya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya iya magance matsalolin Nijeriya a cikin shekara guda da kama mulki.

Sarkin Kano na 14, Muhammad Sunusi II, shi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis sa’ilin da yake jawabi a taron ƙoli na tattalin arziki da zuba jari wanda jihar Rivers ta shirya a Fatakwal, babban birnin jihar.

Sunusi ya ce, “A irin wannan yanayin ya kamata mu fuskanci zahiri a matsayinmu na ‘yan ƙasa, ɓarnar da aka tafka a Nijeriya cikin shekaru 10 wadda ta gurgunta duk wani sashin gudanarwar ƙasar ba za a iya magance ta a watanni shida ko shekara guda ba.”

Dangane da matsalolin tattalin arziki da cire tallafin man fetur ya haifar kuwa, Sunusi ya ce, “Muna buƙatar fahimtar cewa za a ɗauki ɗan lokaci kaɗan kafin mu ga canji da ake fata, amma matakan da aka ɗaukan sun zama dole ne don ceto tattalin arzikin Najeriya.”

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin fetur a watan Mayun bara,’yan Nijeriya suke fukantar tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.

By Editor