…kan karagar Sarkin Kano
…Mun ba tsoffafin sarakuna kwanaki biyu su kwashe komatsansu – Gwamna Abba
Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana Muhammadu Sanusi ll, wanda aka fi sani da Sanusi Lamiɗo Sanusi, a matsayin sabon Sarkin Kano na 16 da zai cigaba da zama karagar mulkin Masarautar Kano.
Gwamna ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da ya ke rattaɓa hannu kan dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, ta yi wa gyara ta shekarar 2019.
Haka kuma Abba Kabir ya ce, a wannan rana ta Alhamis 22 ga Mayu, 2024, na wannan shekarar ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano su ka yi zama na ƙarshe tare da daidaita wannan doka ta Majalisar Masarautu, inda sabuwar dokar ta rushe sababbin masarautun.
“Kasancewar gyaran da aka yi wa wannan doka a yau, sabuwar dokar ta ba mu damar cire sarakunan da tsohuwar gwamnatin son zuciya ta naɗa su biyar ba bisa qa’ida ba,” inji gwamnan.
Gwamna ya ƙara da cewa, tunda wannan doka ta yarda a rusa waɗannan masarautu, su ma a matsayinsu na masu jan ragamar Gwamnatin Jihar Kano sun amince da wannan doka.
Kazalika, gwamnan ya ce, ba tare da vata lokaci ba, yana umartar sarakunan biyar da aka tuve wa rawani su yi gaggawar kwashe kayansu daga gidajen sarautar da suke ciki.
“Mu na kuma ba su umarnin su miqa dukkan wasu kayayyakin gwamnati ga Kwamishinan Ƙananan Hukumomin Jihar Kano, wanda shine mai taimaka wa gwamnan jihar, cikin lokaci.
Gwamna Abba ya kuma buqaci al’ummar jihar su cigaba da yin addu’o’in zaman lafiya ga sabon sarkin da aka maida wa martabarsa tare da farfaɗo da cigaban jihar ga idon duniya.
“Wannan sanin kowane ƙirƙiro wa daancan masarautu babu abinda ya haifar face raba wa al’ummarmu kawuna da koma-baya wajen cigaba,” inji shi.
Abba Gida-gida ya kuma miƙa jinjina ga ’yan majalisar bisa namijin ƙoƙarin da su ka yi wajen sabunta wannan doka, don kauce wa dukkan abubuwan qi da suka zama tarnaƙi ga cigaban al’umma.
Shi ma a nasa jawabin lokacin da Manhaja ta ke tattaunawa da shi bayan kammala jawabin gwamnan, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar ’Yan Gurasa, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, ya ce, wannan doka ita ce dokar da ta ke da kyau tare da inganci.
Lawan Hussaini ya ƙara da cewa, a yau Juma’a ’yan majalisar za su ƙara zama, don samar da wata dokar da za ta iya duba yuwuwar samar da wasu masarautun masu daraja ta biyu.
Sai dai Shugaban Masu Rinjayen ya ce, ba lallai hakan ta yiwu ba, amma za su fara zama, don duba yuwuwar abin.
Wakilin Manhaja ya tambaye shi, ko akwai yuwuwar idan an samar za a cike wancan gurbin, sai ya ce, “ya zuwa yanzu ba ni da wannan amsar har sai abinda zaman na farko zuwa na ƙarshe ya bayar.”
Sai da a wata mai kama da hakan a jiya da safiya ne al’ummar da yawa suka fara bayyana albarkacin bakinsu kan yuwuwar dawo da sarkin mai murabus, inda wasu da yawa suke bayyana cewa, an hango jami’an tsaro sun yi wa Fadar Sarkin kano ƙawanya.
Sai dai yayin da Hukumar Farin Kaya ta DSS ta ji wannan batu na cewar, jami’anta sun zagaye Masarautar Kano, ta yi ƙarin haske, don wanke kanta.
Hukumar Jami’an DSS ta ce, gaskiya ba ta da alaƙa da zagaye fadar Masarautun Jihar Kano tun lokacin da aka fara wannan batu.
Daga ɓangaren al’ummar gari kuwa, da yawan al’umma nata sam-barka tare da kabbara, musamman lokacin da Gwamna Abba Kabir ya bayyana Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin da zai cigaba da riqon sarautar a matsayin mai daraja ta ɗaya.
Gwamna ya kuma yi alƙawarin cigaba da bayar da himma wajen tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano, inda ya yi godiya ga jami’an tsaron da ke jihar bisa gudunmuwar da su ke badawa.
Sannan ya kuma gode wa ’yan jarida da ke aiki babu dare ba rana wajen bayyana wa duniya irin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na cigaban jihar ta Kano.
