24
May
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bai wa jami'an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya wajen yaƙi da ɓarayin daji a faɗin jihar. Ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci taron majalisar tsaron jihar Zamfara a Fadar Gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar. Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwmanan, Sulaiman Bala Idris, taron ya mai da hankali ne kan sha'anin tsaron jihar da kuma yaƙi da ɓarayin daji da ke gudana a jihar. Sanarwar ta rawaito Lawal na cewa, “Taron yau zai auna sha'anin tsaron jihar ne don sanin nasarorin…
