Majalisar Dokokin Kano ta rushe sabbin masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da rushe sabbin masarautu huɗu da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙiro a jihar.

Majalisar ta kuma rage matsayin sarakunan masarautun da abin ya shafa zuwa hakimai.

Masarautun da lamarin ya shafa su ne; Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano.

Majiyarmu ta ce an girke jami’an tsaron hukumar DSS a Fadar Sarkin Kano a safiyar Alhamis da ake soke sabbin masarautun.