Ina son rubutuna ya zama silar sauyin rayuwar wasu – Safiyya Mukhtar Garba

“Satar fasaha ce babba matsalar marubuta”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Safiyya Mukhtar Garba na daga cikin matasan da suke ƙoƙarin tasowa a tsakanin marubutan adabi. Ta fito ne daga Jihar Kano a Ƙaramar Hukumar Gwale. Tun Safiyya na ƴar shekara 13 ta fara nuna sha’awarta ga karatun littattafan Hausa, har ita ma ta kai ga tunanin fara ƙirƙirar nata labarin, sakamakon yadda ta fahimci cewa marubuta suna ba da gudunmawa ne ga gyaran al’umma ta hanyar rubuce-rubuce na hannunka mai sanda da nuni cikin nishaɗi. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa burinta na ganin rubuce-rubucenta sun kawo sauyi a rayuwar mutane da dama.

MANHAJA: Mu fara da jin wacce ce Safiyya Mukhtar Garba?

SAFIYYA: Sunana Safiyya Mukhtar Garba an haife ni a Unguwar Ɗorayi da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a cikin Jihar Kano. Ni marubuciyar littattafan Hausa ce, kuma ɗaliba a Kwalejin Nazarin Shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano. Sannan kuma ina tava kasuwanci da sana’ar saqa, don tun ban kai haka ba Abbana ya ke bani jarin sana’ar saqa na ke yi ta yara jarirai. Ina saƙa hula da safa da kayan sanyi na sayar.

Ko za ki ba mu tarihin rayuwarki da yadda ki ka taso?

Da farko dai, ni haifafiyar Jihar Kano ce daga Ƙaramar Hukumar Gwale. Daga baya aiki ya mayar da mahaifina Ƙaramar Hukumar Ƙiru, inda muka koma Kwanar ɗangora da zama. Na yi karatuna na firamare a makarantar Hayatul Islam, na kuma yi Sakandiren ‘Yammata ta Gwamnati (GGASS) a Kafin Maiyaƙi. Na kuma shiga Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta CAS da ke Tudun Wada. Yanzu haka kuma ina Kwalejin Nazarin Shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano da ke garin Kano, ina karantar Harshen Hausa da Larabci. Sannan kuma na yi karatuna na Islamiyya da Tahfiz, inda na yi sauka duk a makarantar Hayatul Islam.

Wacce gwagwarmaya ki ka fuskanta a lokacin tasowarki da ya inganta rayuwarki zuwa yanzu?

Tabbas rayuwa tana cike da ƙalubale da faɗi tashi, amma duk da haka babu abinda zan ce wa Allah sai godiya. Na samu tarbiyya daga dattijan iyayena irin ta addinin Islama da kuma kulawa. Sun tsaya tsayin daka domin ganin na yi ilimin da zai amfani rayuwata ko da ransu ko babu. Wanda ta dalilinsa har ya sa na fara tunanin me zan ƙiƙira da zan tura shi ga al’umma har su ilmantu? Shi ne ya sa na rungumi rubutu don faɗakar da jama’a wasu darussa na rayuwa, a irin tawa fahimtar.

Wanne buri ne ki ka taso da shi a rayuwarki wanda har yanzu ki ke son ki ga kin cimma?

A gaskiya na taso ina mai matuƙar sha’awar duk wani abu da ya danganci aikin jarida, ko karanta labarai da littattafai kamar yadda ake yi a rediyo ko a YouTube. Ko kuma in ƙirƙiro da labari na rubuta a matsayin littafi. Don haka tun ina qarama nake da matuqar sha’awar wannan harkar a raina, kodayake har kawo yanzu burina bai kai ga cika ba, amma ina kan hanya. Ba da jimawa ba ma akwai gidan wata jarida na onlayin a Zariya da suka nemi in riqa karanta musu labarai a tashar su mai suna HZAN News Nigeria, har mun fara amma daga baya aka rufe tashar. Sannan kuma ina son na fara aikin ɗora murya na finafinan ƙasashen ƙetare ɗin nan, irin wanda ake nunawa a tashar Hijra TV, nan ba da daɗewa ba, in sha Allah. Wannan shi ne abin da na taso da shi a raina, kuma nake da burin cimma a rayuwata.

Me ya ja hankalinki ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Abinda ya ja hankalina na fara tunanin zama marubuciya bai wuce yawan karance-karancen littattafan Hausa ma magabatan marubuta ba. Yadda nake ganin suna tsara labari, sai nake ganin ni ma me zai hana na gwada tawa sa’ar? Na ga ko zan iya. Sai na ga masha Allah, ashe zan iya ɗin saboda da koyo ake zama gwani.

Waye ya fara taimaka miki da shawarwari kan yadda za ki fara rubutu, kafin ki fahimci yadda al’amura suke?

Na tambayi marubuta da dama lokacin da zan fara rubutu wasu su bani amsa wasu kuma akasin haka. A ƙarshe dai na haɗu da wata baiwar Allah, Batul Adam Jattako, wacce ta buɗe min komai ta hanyar nuna min yadda zan yi. Sannan na haɗu da Nazifa Sabo Nashe da ta yi min hanyar shiga ƙungiyar Mikiya Writers’ Association. Kafin nan ma na shisshiga wasu ƙungiyoyin marubuta daban-daban, domin ƙara samun ƙarin haske akan hakan, yadda zan inganta rubutuna.

Wanne abu ne ya sa ki ka tsaya a ƙungiyar Mikiya, akwai wani abu da ya ke birgeki ne?

Ba wai don tana ƙungiyata ba, Mikiya ƙungiya ce da ta amsa sunanta, ta fita zakka a tsakanin sauran ƙungiyoyin marubuta. Da farko ana nuna wa sabbin marubuta hanyar da za su bi su gane muhimmancin shi kansa rubutun. Da yadda za a koya musu yadda ake zaɓar salo da jigo wajen zubin labari. Ba iya nan ba, ana gabatar da shirye-shirye da za sa su fahimci yadda ake rubutu da asalin kalmar adabi.

Sannan a Mikiya Writers muna ƙirƙirar gasa a tsakanin mambobin domin ƙarawa iliminsu akan gasar rubutun gajerun labarai na cikin ƙungiya, don su koyi yadda za su shiga gasar gajerun labarai da ake shiryawa duk shekara, a ƙungiyoyi da cibiyoyin ilimi daban-daban. Mikiya na yaɗa littattafan ƴaƴanta, domin ya je inda ba su yi zato ba. Kuma Allahamdulillahi hakan abin birgewa ne matuƙa.

Musamman yadda mutum zai zo da labarinsa a bashi shawara ko a sauya labarin gabaɗaya. Babban abin birgewa a ƙungiyar Mikiya shi ne muna da haɗin kan da idan matsala ta samu wani mamba ta kuɗi ko ta wata lalura, za mu zo mu tattauna mu ga yadda za mu taimaka, sai mu saka gidauniya. Hakan yana taimakawa mambobin cikinta sosai. Sannan muna ƙoƙari sosai wajen ganin mun daidaita Hausar kowa, don ta ta fi da asalin daidaitacciyar Hausa da ya kamata kowanne marubuci ya yi amfani da ita.

Za ki iya tuna labarin farko da ki ka rubuta, akan mene ne, kuma shin kin iya fitar da shi ga masu karatu?

Littafina na farko shi ne ‘Saqar Zare’, wanda yake ɗauke da jigon labarin da ya shafi cin amana da yaudara, ba wai a tsakanin saurayi da budurwa ba, a’a, a tsakanin ɗa da mahaifi. Kuma tabbas na fitar da shi ga masu karatu.

Daga lokacin da ki ka fara rubutu zuwa yanzu, mene ne ya canza daga yanayin salon rubutunki, da gogewarki wajen kula da ƙa’idojin rubutu?

Gaskiya an samu banbance-banbance a rubutuna musamman ta fuskar ƙa’idojin rubutu. Saboda ya kasance ɓangarena ne a karatuna da nake yi da kuma ina sake samun dabarun shimfiɗa labari da inganta ginuwarsa ta yadda masu karatu da dama ke yabawa.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa? Ba mu sunayensu da bayanin fitattu 3 daga ciki.

Ban rubuta litattafai masu yawa ba, idan na haɗe duk da gajerun labaran da na rubuta aƙalla ina da labarai sun kai shida. Akwai ‘Saqar Zare’ da ‘Auren Sadaka’ sai kuma ‘Madiha’.

Littafin ‘Saƙar Zare’ yana ƙunshe ne da labarin wata yarinya wacce take zaton mahaifinta ne ya sace ta daga asibiti tun tana jaririya, domin cimma wata manufarsa a kanta, don samun damar shiga ƙungiyar asiri. Labari ne na yadda uba da ƴa suke dambarwa, da yadda zargi, da mugunta, da cin amana suke haddasa gagarumar fitina a cikin wannan iyali. Yana kuma ɗauke da darussa da dama da suka haɗa da ribar haƙuri, imani da ƙaddara, da kuma illar shiga ƙungiyoyin asiri.

Shi kuwa littafin ‘Auren Sadaka’, littafi ne da ya ƙunshi labarin wani nakasasshen bawan Allah kuma talaka fitik wanda ba shi da cin yau ba shi da na gobe. Sai ƙaddara ta same shi aka aura masa wata yarinya ƴar masu kuɗi a matsayin sadaka aka bashi, saboda wani rikicin ƴan ubanci da ya tashi a gidansu da zarginta da ake yi. Wannan ne ya haifar da rikita-rikitar da ke ƙunshe a labarin wacce har ta kai ga an yi ta kai ruwa rana tsakaninta da mijinta Malam Hudu, da yadda hakan ya yi matuƙar dagula lissafin rayuwarta, na abinda ba ta tava zata ba kuma ba ta tsammata ba.

Shi kuma littafin ‘Madiha’ labari ne mai ɗauke da wata ƙullalliyar harƙalla game da abinda ya shafi tsaro, ɗaukar fansa, cin amana, soyayya da kuma ta’addanci. Wanda hakan ya kawo sauyi mai matuƙar yawa a cikin labarin ga manyan taurarinsa.

Wanne littafin ne a cikinsu ya fi wahalar da ke wajen rubutu, da wanda ki ka fi samun sauƙinsa? Mene ne ya kawo haka?

Littafin ‘Saƙar Zare’ shi ya fi wahalar da ni saboda shi ne rubutuna na farko, kuma salon da na ɗauko yana da tsauri, mai salon tafiyar kura ne. Amma littafin da ya fi min sauqin rubutawa shi ne ‘Auren Sadaka’. Rubutunsa ya yi min daɗi saboda duk sanda zan rubuta ina cikin shauƙi nake rubuta shi.

Kina yin littafin kyauta ne ko na kuɗi? Kuma wanne ne ki ka fi samun alheri a ciki?

Ina yin na kuɗi da kuma na kyauta. Sai dai wanda na yi na kyauta na fi samun mabiya a cikinsa. Na kuɗi shi ma ina samun mutane, amma shi kuma zan ce na fi samun alheri a kansa.

Wasu marubuta na yin rubutu ne daga abin da ya faru da su ko wasu na kusa da su, ko kuma ƙirƙira bayan kallon wani fim ko karatun littafi, ke daga ina ki ke samo jigon labaranki?

Ina iya samun jigo a ɓangarori da yawa. Ko a tafe ko a cikin hira ina iya tsintar jigo a ciki. Musamman game da abinda yake faruwa a rayuwar yau da kullum. Babu wani waje guda ɗaya.

Wanne lokaci ne ya fi miki daɗi in za ki yi rubutu?

Na fi jin daɗin yin rubutu da daddare, lokacin da gari ya yi shiru babu hayaniya.

Yaya ki ke kallon matsalar satar fasaha a tsakanin marubuta, shin an tava sace miki labari, ko an karanta a YouTube ba da izininki ba?

Wannan matsalar tana ci mana tuwo a ƙwarya mu marubuta. Tabbas kuma abin kamar ya zama ruwan dare, duk da ni ba a tava gwada min ko ɗaya ba, amma ana yi wa ƴan uwana ina gani. Wata sunayen mutane da na labarin kawai za ta canza, sai ta ɗora labari ta ce nata ne.

Marubuta da dama suna fitar da littattafansu a YouTube ko su sayar wasu su karanta, shin wanne ki ka fi yi?

E, ni ma na fitar da nawa an karanta a YouTube, duk da yawanci masu karanta littafi a YouTube ɗin sun fi tambayar a ba su littafi kyauta su karanta, a maimakon su biya kuɗi su karɓa.

Tsakanin sanya littafi a manhajojin sayar da littafi, irinsu Hikaya da Arewabooks, da ɗorawa a YouTube ko sayarwa ta WhatsApp, wanne aka fi samun kuɗi a ciki?

Dukkansu ana samun kuɗi. Amma zan iya cewa an fi samu a ɗorawa a YouTube, saboda shi za a bai wa mutum kuɗinsa ne a dunƙule.

Waɗanne hanyoyi ki ke ganin marubuta za su bi don inganta kasuwancin littattafansu?

Hanyoyin inganta kasuwancin littafi musamman na onlayin bai wuce mutum ya riƙa adana littafinsa a manhajojin Hikaya Bakandamiya, da irinsu Arewabooks, inda zai ba su tsaro da kariya ta musamman.

Kin taɓa buga littafinki a takarda, ko sai a onlayin kawai ki ke fitar da su?

A’a, ban tavia ba gaskiya. Iyakacina a onlayin nake sakewa. Amma ina da burin haka kuma nan gaba idan Allah Ya so.

Faɗa mana sunayen marubuta uku maza da mata da ki ke kallo a matsayin allon kwaikwayonki ta fuskar rubutu?

Akwai Batul Adam Jattako, akwai Fauziyya D. Sulaiman, sannan akwai Jibril Adam Jibril Rano.

Mene ne burin da ki ke so ki cimma nan gaba a fagen rubutu?

Burina bai wuce na kai matakin nasara a rubutu ba. Ina son in samu damar da zan taimakawa ƴan uwana marubuta, kuma ya zama a dalilin rubutuna a samu kawo sauyi ko ta fuskar kiwon lafiya ko tsaro ko makamancin haka.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Da wuya ta kashe ni gwara daɗi ya kasheni. Saboda wuyar nan babu daɗi, shi kuma kisan daɗi ai daɗin ne da ya yi daɗi daga baya yake zama wahala (dariya).

Na gode.

Ni ma na gode.