Yanzu-yanzu: Kotu ta ba da belin Abba Kyari

A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin DCP Abba Kyari, na mako biyu.

Kotu ta ba da belin ne don bai wa Kyari damar zuwa kammala jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu.

Kazalika, Kotun ta tsayar da ranar Juma’a, 31 ga Mayu a matsayin ranar da za ta yi matsaya kan buƙatar belin da Kyari ya gabatar mata.

Idan ba a manta ba, Kyari na fuskantar shari’a ne kan tuhume-tuhume masu nasaba da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA.