Cikar Tinubu shekara guda kan mulki: Babu wani bukin a-zo-a-gani da za a shirya —Idris

Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, ba za a shirya wani biki na a-zo-a-gani ba don cikar Shugaba Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulkin Nijeriya.

Idris ya shaida wa manema labarai haka ne ranar Laraba a Abuja.

A cewar Ministan, an ɗauki wannan mataki ne don cika manufar Tinubu ta yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata da kuma yin amfani da dukiyar ƙasa don amfanin ‘yan ƙasa.

Ya ce, “bukin ba zai zama ƙasaitacce ba, illa iyaka za a bai wa ma’aikatu damar yin bayani kan ayyukansu.

“Wannan ya yi daidai da manufar gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da tafiyar da dukiyar ƙasa don amfanin ‘yan ƙasa.

“Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin a ba da muhimman bayanai ta gaskiya kuma a lokacin da ya dace,” in ji Idris.

Ya ƙara da cewa, ana buƙatar kafafen yaɗa labarai su zamo masu gaskiya a harkokinsu da kuma kwatanta kishin ƙasa.