Babu sarki a Kano a halin yanzu — Majalisa

Biyo bayan soke masarautun da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ƙirƙiro a Kano a zaman da ta yi ranar Alhamis, Majalisar Dokokin Jihar ta ce a halin yanzu babu sarki a Kano.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske dangane da matakin rushe masarautun da majalisar ta ɗauka.

Ya ce a halin da ake ciki an aike da dokar masarautun da aka yi wa kwaskwarima ga Gwnan Kano, Abba Kabir, don ya rattaɓa hannu.

Ya kara da cewa, dokar ta bai wa Gwamna dama ya kira masu zaɓen sarki don su zaɓi wanda ya fi cancanta ya zama sarkin Kano.

Sai dai, alamu na nuni da cewa, akwai yiwuwar a dawo da tsohon sarkin da Ganduje ya tsige kuma tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido, kan kujerar sarautar masarautar ta Kano.

Masarautun da Majalisar ta rushe a zamanta na ranar Alhamis su ne Masarautun da lamarin ya shafa su ne; Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano.