Editor

9513 Posts
Tsaro: Shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshi

Tsaro: Shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshi

Daga Umar Gombe Bayanan da jaridar Manhaja ta samu daga Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, sun nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin sojin Nijeriya. Wadanda nadin ya shafa su ne; Major General Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaron kasa da Maj. Gen. I Attairu a matsayin babban hafsan sojojin kasa, sai A Z Gambo a matsayin babban hafsan sojojin ruwa da kuma AVM IO Alao a msatsayin babban hafsan sojojin Sama. Kafin wannan lokaci, 'yan Nijeriya da dama sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan bukatar da ke akwai na yi wa shugabannin sojoji garambawul don inganta…
Read More
“Filayen Nijeriya mallakar jihohi ne ba na Fulani ba” – Sanata Jibrin

“Filayen Nijeriya mallakar jihohi ne ba na Fulani ba” – Sanata Jibrin

Daga Fatuhu Mustapha An yi kira ga al'umar Fulani a fadin Nijeriya da su rungumi zaman lafiya da sauran kabilu tare da bai wa gwamnatocin jihohi hadin kai wajen yaki da ta'addanci. Sarkin Fulanin jihar Nasarawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar yau Talata. Jaridar Manhaja ta ruwaito Sanata Jibrin na cewa, "Ba na tare da duk wanda ke ra'ayin Fulani ne ke da mallakar filayen Nijeriya. Jihohi su ke da mallakar filaye." Sarkin Fulanin ya yi kira ga 'yan Nijeriya, musamman gwamnoin Ondo da Oyo da…
Read More
COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin saukaka dokar kulle

COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin saukaka dokar kulle

Daga jaridar Manjaha Gwamnatin Tarayya ta sanar da saukaka dokar kulle a karo na uku, inda ta kara wa'adin dokar da wata guda. Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da Cutar Korona (PTF) ne ya bayyana haka a Litinin da ta gabata a Abuja, yayin da yake gabatar da rahoton ayyukansa na mako-mako kamar yadda ya saba. Da yake jawabi, shugaban kwamitin Boss Mustapha ya ce, "PTF na nan na kokarin inganta sha'anin tafiye-tafiye zuwa ketare domin takaita kalubalen da matafiya kan fuskanta. “Haka nan, kwamitin na nazarin matakan sassauta dokar kulle karo na uku kasancewar wa'adin dokar da aka sanya…
Read More